'Yan Bindiga Sun Sace Matafiya Kusan 20, Sun Nemi a Biya Sama da Naira Miliyan 500

'Yan Bindiga Sun Sace Matafiya Kusan 20, Sun Nemi a Biya Sama da Naira Miliyan 500

  • Wasu mahara sun yi wa motar bas kwantan ɓauna, sun sace fasinjoji 18 tare da direba a jihar Ekiti a ranar Lahadi
  • Wata majiya ta ce biyu daga cikin fasinjojin sun gudo daga hannun ƴan bindigar a lokacin da suke tafiya a cikin daji
  • An tattaro cewa maharan sun fara kiran iyalan waɗanda suka sace suna neman kuɗin fansa Naira miliyan 30

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Wasu ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi wa wata motar bas mai dauke da fasinjoji 18 kwanton bauna a Emure Ile.

Ƴan bindigar sun yi awon gaba da dukkan fasinjojin motar waɗanda ke hanyar zuwa Ado-Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Sufetan yan sanda.
Yan bindiga sun sace matafiya kusan 20, sun nemi kowane a biya N30m Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Lamarin ya faru ne a gefen garin Emure-Owo kan iyakar jihohin Ekiti da Ondo, a lokacin da motar bas din ke dawowa daga Onitsha ranar Lahadi, Tribune ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ajali ya yi: Wata tirela ta murkushe mai adaidaita sahu, bayin Allah sun rasu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace matafiya 18

Wata majiya a kungiyar ma’aikatan sufuri ta RTEAN reshen tashar motar Ado-Ekiti ta ce ‘yan bindigar sun yi garkuwa da direban mai suna Sunday Emmanuel tare da sauran fasinjojin.

Majiyar wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce maharan sun bar yara a cikin motar, kuma kukansu ne ya ja hankalin masu wucewa da sanyin safiyar jiya.

A cewarsa, ganin kananan yara a motar ya ja hankalin mazauna yankin suka yi gaggawar kai rahoto caji ofis na ƴan sanda mafi kusa.

'Yan bindiga sun nemi fansar N30m

A rahoton The Nation, mutumin ya ce:

"Sun ja motar zuwa cikin daji sannan suka kwashe dukkan fasinjoji, sun kira ƴan uwan direban motar kuma sun nemi fansar Naira miliyan 30. Sun ce za su sake kira amma har yanzu shiru."

Majiyar ta kuma bayyana cewa biyu daga cikin fasinjojin motar sun gudo daga hannun maharan a lokacin da suka tasa su zuwa cikin daji.

Kara karanta wannan

Bidiyon lokacin da jirgin kasa ya murkushe wata mota a Legas, mutane sun magantu

Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar sun nemi a biya N30m a matsayin kuɗin fansar kowane mutun ɗaya, jimulla kuɗin sun haura N500m.

Yan sanda sun kubutar da mutane a Taraba

A wani labarin, kun ji cewa yan sanda sun yi nasarar kubutar da mutanen da ƴan bindiga suka yi yunkurin garkuwa da su a jihar Taraba.

Ƴan bindigar sun gamu da turjiya daga ƴan sanda ne bayan sun shiga garin Sibre, sun ɗauki mutane da nufin tafiya da su cikin daji.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262