"Akwai Kura Kurai": Shugaba Tinubu Ya Tabo Batun Bincikar Hafsoshin Tsaro

"Akwai Kura Kurai": Shugaba Tinubu Ya Tabo Batun Bincikar Hafsoshin Tsaro

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed ya yi magana kan bincikar yadda hafsoshin tsaro ke kashe kuɗaɗen da ake ba su
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa ba zai binciki hafsoshin tsaron ba waɗanda ya naɗa bayan hawansa mulki
  • Shugaba Tinubu ya nuna cewa duk da akwai ƴan kura-kurai yana alfahari da aikin da suke yi a ƙasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi magana kan batun bincikar hafsoshin tsaro.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa ba zai binciki hafsoshin tsaro ba, inda ya jaddada cewa ba abu ba ne mai kyau rashin mutunta hukumomin da suke jagoranta.

Tinubu ya yi magana kan bincikar hafsoshin tsaro
Shugaba Tinubu ba zai binciki hafsoshin tsaro ba Hoto: @SundayDareSD, @ubasanius
Asali: Twitter

Shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambayoyi a hirar da ya yi da ƴan jarida a daren ranar Litinin a cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

"Babu tausayi": Kusa a PDP ya caccaki Tinubu, ya fadi halin da ya jefa 'yan Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Tinubu ya ce kan bincikar hafsoshin tsaro?

Da aka tambayi Shugaba Tinubu kan yadda hafsoshin tsaro ke amfani da ƙudade wajen yaƙi da ta’addanci da sauran ƙalubalen tsaro a ƙasar nan, Tinubu ya ce ya gamsu da irin ayyukan da suke yi.

"Ba zan binciki hafsoshin tsaro ba. Ba zai yiwu a ƙi mutunta hukumomin da barazanar bincike ba, ba za a iya yin nasara a wannan yaƙin ba tare da saka hannun jari a fasaha, makamai da horo ba."
"Akwai yuwuwar samun ƴan kura-kurai a nan da can amma ba da yawa ba. Mun sanya ido kan yadda ake fitar da kasafin kuɗin mu da kuma yadda ake kashe su."
"A yi la'akari da jin daɗin sojojinmu maza da mata, suna aiki a cikin yanayi mai tsanani. Muna da ƙasa mai girman gaske, mai daji da yawa da wuraren da ba kowa."
"A yaba musu kan abin da suke yi, ina alfahari da abin da suke yi a yau, ba buƙatar a yi bincike."

Kara karanta wannan

Rikicin sarauta ya ƙara tsananta, gwamna ya fusata, ya soke naɗin sabon sarki

- Bola Tinubu

Tinubu ya magantu kan tsadar lantarki

A baya rahoto ya zo cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba ƴan Najeriya mafita kan tsadar da wutar lantarki ta yi a ƙasar nan.

Mai girma Bola Tinubu ya shawarci ƴan Najeriya da su riƙa sanya lura kan yadda suke amfani da wutar lantarki, ya buƙaci da su riƙa kashe fitilu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng