Yadda Babban Ɗan Jarida Ya Shirya Yi wa Tinubu Ƴar Ƙure Amma Wani Dalili Ya Hana

Yadda Babban Ɗan Jarida Ya Shirya Yi wa Tinubu Ƴar Ƙure Amma Wani Dalili Ya Hana

  • Reuben Abati ya bayyana yadda Shugaba Bola Tinubu ya nuna kwarin gwiwa a tattaunawarsa da 'yan jarida a Legas
  • Dan jaridar ya ce Tinubu ya amsa tambayoyi cikin natsuwa duk da cewa bai san tambayoyin da aka shirya masa ba
  • Abati ya yi bayanin yadda ya so titsiye Tinubu a lokacin da ake tattaunawar amma wani babban dalili ya hana shi yin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Tsohon hadimin shugaban kasa kuma mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin, Reuben Abati, ya bayyana abin da ya wakana a tattaunawa da shugaba Bola Tinubu.

Da yake magana a ranar Talata, Abati ya ce shugaba Tinubu ya nuna kwarin guiwa da kwarewa yayin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jaridar.

Ruben Abati ya yi magana kan tattaunawarsu da Shugaba Bola Tinubu
Ruben Abati ya fadi yadda Tinubu ya amsa tambayoyin 'yan jarida cikin nutsuwa. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Reuben Abati na daya daga cikin 'yan jarida bakwai da suka yi hira da shugaba Bola Tinubu a gidansa na Ikoyi, jihar Legas a ranar Litinin, inji rahoton Arise News.

Kara karanta wannan

'Ku yi mani addu'a': Tinubu ya roki yan kasa bayan jawabinsa da ya fusata al'umma

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya amsa tambayoyi cikin nutsuwa

Abati ya bayyana cewa ba a nemi ‘yan jarida su mika tambayoyi kafin tattaunawar ba, kuma ba a tattauna komai da shugaban kasar kafin zaman ba.

A cewar dan jaridar:

“Na ji dadin yadda ya yi magana cikin kwarin gwiwa, yana nuna cewa ya kware kan aikin nasa, kuma ya san abin da yake yi.”

Abati ya kara da cewa:

“Na yi mamakin yadda ya zo ya zauna dakin hirar ba tare ya yi wani shiri ba, kuma ya zo ya yi magana cikin kwarin gwiwa da sanin makamar aiki.”

Dan jarida ya so ya titsiye Tinubu

Vanguard ta rahoto Abati ya bayyana yadda Tinubu ya yi magana cikin natsuwa, inda yake amsa tambayoyi ba tare da wani rudani ba, duk da cewa ba su gana kafin zaman ba.

"Na so na yi masa wasu 'yan tambayoyi domin kure shi, irin tambaya daya zuwa biyu haka. Amma abin mamaki, yana zaune ko gezau."

Kara karanta wannan

El Rufai, Shetty da mutane 17 da Tinubu ya ba mukamai amma daga baya ya soke nadin

Abati ya ce akwai bukatar shugaba Tinubu ya ci gaba da irin wannan tattaunawar a kai-a kai domin ya bayyana wa ‘yan Najeriya manufofinsa kai tsaye.

Tinubu ya magantu kan tsadar wuta

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya ba 'yan Najeriya satar amsar yadda za su rage biyan kudin wutar lantarki da suke sha.

Shugaba Tinubu ya ce akwai bukatar 'yan Najeriya sun san lokutan da za su rika kashe fitilu da sauran kayan da ke jan wuta a lokacin da ba sa amfani da su.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.