An Tura Tsohuwar Matar Sarki Kurkuku kan Mutuwar Yara a Makarantar Musulunci
- Babbar Kotun Majistare a Ibadan ta bayar da umarnin tsare wasu mutane uku, ciki har da shugaban makarantar Musulunci ta Bashorun
- Tsohuwar matar Ooni na Ife, Naomi Silekunola da mai gidan rediyon Agidigbo FM, Alhaji Oriyomi Hamzat sun kasance cikin wadanda aka tsare
- Hakan na zuwa ne yayin da ake zarginsu da hannu kan jawo mutuwar yara da dama a makarantar Musulunci ta Boshorun a jihar Oyo
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Oyo - Babbar Kotun Majistare da ke Iyaganku a Ibadan ta yanke hukuncin tsare wasu mutane uku dangane da hatsaniyar da ta faru a makarantar Musulunci ta Boshorun.
Mutanen sun hada da shugaban makarantar, Abdullahi Fasasi; mai gidan rediyon Agidigbo FM Alhaji Oriyomi Hamzat; da kuma tsohuwar matar Ooni na ife, Naomi Silekunola.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa an yanke hukuncin ne bayan gurfanar da su a gaban kotun da ‘yan sandan jihar Oyo suka yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Laifin da ake zarginsu da aikatawa
Lauyan masu kara ya gabatar da tuhuma hudu a gaban kotun, ciki har da saba dokar sashe na 324 na kundin manyan laifuffuka na jihar Oyo.
An ce wadanda ake tuhumar suna da hannu a hatsaniyar da ta yi sanadiyyar mutuwar wasu yara da dama a makarantar Musulunci ta Bashorun
Mai shari’a Olabisi Ogunkanmi ya yi bayanin cewa za a tsare su a gidan gyaran hali na Agodi, yayin da ake jiran karin bayani.
An samar da tsaro lokacin shari'ar
An gudanar da zaman kotun ne karkashin tsauraran matakan tsaro, inda iyalai da sauran mutane masu sha’awar ganin yadda za a kaya suka yi cincirindo a wajen kotun.
Ana ganin cewa matakin tsaron ya kasance wajibi duba da girman hatsaniyar da ta faru a makarantar, wanda ya jawo hankalin jama’a sosai.
Premium Times ta wallafa cewa kotun ta dage sauraron karar har zuwa lokacin da za a samu karin bayani daga masu gabatar da kara.
Makinde ya yi jimamin hadarin yara a Oyo
A wani rahoton, kun ji cewa gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya yi alkawarin hukunta duk wanda aka samu da laifi a turmutsistin yara a Ibadan.
Gwamna Seyi Makinde ya yi ta'aziyya ga wadanda suka rasu yayin turmutsitin inda ya ce lamarin abin tashin hankali ne matuka.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng