'Ku Yi Mani Addu'a': Tinubu Ya Roki Yan Kasa bayan Jawabinsa da Ya Fusata Al'umma

'Ku Yi Mani Addu'a': Tinubu Ya Roki Yan Kasa bayan Jawabinsa da Ya Fusata Al'umma

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci 'yan Najeriya su rungumi kaunar juna, zaman lafiya da hadin kai yayin bikin Kirsimeti na bana
  • Tinubu ya jaddada muhimmancin addu'a da goyon bayan shugabanni don ciyar da Najeriya gaba tare da jawo hankali kan jinƙai ga marasa ƙarfi
  • Ya yaba wa sojojin Najeriya kan jajircewarsu, yana tabbatar wa 'yan ƙasa da cewa gwamnati na aiki domin inganta rayuwar al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi kira ga 'yan Najeriya su taya shugabanni da addu'a domin samun nasara.

Tinubu ya ce ya kamata yan kasar su rungumi kaunar juna da zaman lafiya da hadin kai yayin bikin Kirsimeti na wannan shekara.

Tinubu ya roki yan Najeriya addu'o'i
Bola Ahmed Tinubu ya roki yan Najeriya addu'o'i domin samun cigaba a kasa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Kirsimeti: Bola Tinubu ya ja hankalin yan Najeriya

Tinubu ya bayyana haka ne a jihar Lagos yayin taya yan Najeriya murnar bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Radadin cire tallafi: Tinubu ya fadi yadda abokinsa ya gagara rike manyan motoci 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ya bayyana wannan lokaci na bikin Kirsimeti a matsayin na tunawa da koyarwar Yesu Kiristi.

Tinubu ya bayyana muhimmancin Kirsimeti a matsayin cikar annabci, tare da jan hankali kan hadin kai da juriya a matsayin ginshiƙan al'umma.

Har ila yau, Tinubu ya nuna alhini kan bala'o'in da suka faru a Ibadan, Okija da Abuja, inda rayuka da dama suka salwanta.

"Tunanina na ga waɗanda har yanzu suke cikin damuwa musamman iftila'in da ya faru."

- Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya bukaci hadin kai a kasa

Tinubu ya jaddada muhimmancin kyautata wa juna, musamman ga marasa galihu, yayin da ya nuna alhini ga iyalan da bala'o'in shekarar nan suka shafa.

Ya yaba wa sojojin Najeriya kan sadaukar da rayukansu domin tsaron ƙasar, yana cewa suna da buƙatar addu'o'i da cikakken goyon baya.

Shugaban ya tabbatar wa 'yan ƙasa cewa gwamnati ta himmatu wurin kawo ababan more rayuwa, cewar Punch.

Kara karanta wannan

'Ku koyi rayuwa a haka': Tinubu ya ba yan Najeriya satar amsa kan tsadar wutar lantarki

Tinubu ya magantu kan rage Ministoci

Kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu ya musanta batun rage yawan ministoci a gwamnatinsa, ya ce kowane da aikin da ya rataya a wuyansa.

Majalisar zartarwa ta gwamnatin Bola Tinubu mai kimanin ministoci 50 ita ce mafi girma da aka taɓa yi a Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.