Kwanaki da Tafiyar Tinubu Legas, An Jibge Jami'an Tsaro a Birnin Tarayya Abuja
- An jibge jami’an tsaro a birnin tarayya domin dakile duk matsalolin tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara
- An rahoto cewa ‘yan sanda sun tura jami’ai 3,180 zuwa wuraren ibada da wuraren tarurruka don tabbatar da tsaro a babban birnin Abuja
- Kwamishinan ‘yan sanda ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin jama’a da hukumomi don samun tsaro a lokacin bukukuwa masu zuwa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gabanin bukukuwan Kirsimeti da abuwar Shekara, an kara matakan tsaro a babban birnin tarayya (FCT), Abuja da sauran jihohin kasar nan.
Tun daga karshen makon da ya gabata, hukumomin tsaro suka fara tura jami’ai don dakile duk wata matsalar tsaro yayin bukukuwan.
An jibge jami'an tsaro a birnin Abuja
Jami'an tsaro sun bukaci ‘yan kasa da su kasance masu sa ido da kuma yin taka-tsantsan a wannan lokaci na bukukuwa, inji rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A Abuja, kwamishinan ‘yan sanda, Olatunji Disu, ya ce an tura jami’ai 3,180 zuwa wuraren ibada don tabbatar da tsaro yayin bukukuwan Kirsimeti.
Yayin da aka gargadi jama'a kan aikata laifuffuka, CP Disu ya ce wannan matakin zai taimaka wajen kara tsaro a wuraren ibada da wajen tarurrukan jama'a.
'Yan sanda sun shirya dakile matsalar tsaro
Ya ce jami’an sashen kai daukin gaggawa, RRS da dakaru na musamman za su gudanar da binciken motoci, sintiri da sauran ayyukan tabbatar da tsaro.
Kwamishinan ya kara da cewa tawagar dakile tashin bam, EOD za ta duba gine ginen gwamnatin tarayya da muhimman gine-ginen jama’a don tabbatar da tsaro.
Ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin ‘yan sanda, shugabannin addinai, da masu wuraren nishadi wajen tabbatar da tsaro a bukukuwan karshen shekarar.
NSCDC ta tura jami'ai 1850 zuwa Kogi
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta tura jami'anta 1,850 zuwa Kogi domin tabbatar da tsaro a Kirsimeti da bikin sabuwar shekara.
Abdullahi Aliyu, mai magana da yawun hukumar a Kogi, ya shaida cewa an tura jami'an ne zuwa wuraren bauta, da inda aka san za a yi tarurrukan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng