'Yan Bindiga Sun Harbe Jariri Dan Shekara 1 da Mutane da Dama

'Yan Bindiga Sun Harbe Jariri Dan Shekara 1 da Mutane da Dama

  • Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai farmaki a Ri Do, karamar hukumar Riyom a jihar Filato, suka kashe mutane 15
  • Kungiyar Irigwe Development Association ta yi kira ga hukumomin tsaro su dakatar da irin waɗannan hare-hare marasa dalili
  • An ruwaito cewa daga cikin wadanda aka yi wa kisan gilla akwai jariri dan shekara daya kuma har yanzu jami'an tsaro ba su ce komai ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Filato - Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a garin Ri Do, wanda aka fi sani da Gidan Ado a karamar hukumar Riyom ta jihar Filato.

Farmakin ya faru a daren Lahadi kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Kara karanta wannan

Zanga zanga: Amnesty ta yi zargin ana son 'karasa' matashin da 'yan sanda suka jefawa gurneti

Filato
'Yan ta'adda sun kashe jariri a Filato. Hoto: Legit
Asali: Original

Rahoton Channels Television ya nuna cewa Kungiyar Irigwe Development Association ta bayyana cewa an kai harin ne ba tare da wani dalili ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harbe jariri da wasu mutane a Filato

Kungiyar Irigwe Development Association (IDA) ta bayyana a wata sanarwa da ta fitar a Jos cewa an kai wani hari da ya shafi al’ummar Irigwe da ke zaune a yankin Bassa.

Sanarwar da Sakataren yaɗa labaran kungiyar, Sam Jugo, ya fitar ta ce harin ya faru ba tare da wani dalili ba, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 15 ciki har da jariri mai shekara daya.

Kungiyar ta yi kira ga hukumomin tsaro su binciki lamarin sosai, tare da tabbatar da cewa an hana maimaita irin wannan hari a nan gaba.

An hana daukar fansa bayan harin yan bindiga

Vanguard ta wallafa cewa kungiyar IDA ta kuma yi gargadi kan daukar fansa, tare da jaddada muhimmancin bin doka da oda wajen magance irin wannan matsala.

Kara karanta wannan

Yunwa ba kyau: Yan bindiga sun tare hanya, sun kwace kayan abincin Kirsimeti a Kaduna

Duk da haka, har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, hukumomin tsaro irin su 'Operation Safe Haven' da 'yan sanda ba su ce komai ba kan harin.

An yi wa mutanen da suka rasa rayukansu jana’izar hadin gwiwa a makabartar garin, yayin da al’ummar yankin suka nuna damuwarsu kan lamarin.

Sojoji sun wargaza wuraren tsafi a Enugu

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa 'yan ta'addar kungiyar IPOB sun gamu da fushin hukuma yayin da sojoji suka musu dirar mikiya.

Sojojin sun kai farmaki wata maboyar wani shugaban IPOB inda suka fatattake su suka wargaza wani waje da suke tsafi domin neman kariya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng