Gwamnan APC Ya Bijirewa Umarnin Gwamnatin Tinubu, Ya Rantsar da Ciyamomin Riko
- Gwamnan Edo ya rantsar da ciyamomin riko, duk da matsayar gwamnatin tarayya kan 'yancin shugabannin kananan hukumomi
- Rantsar da shugabannin rikon ya jawo ce-ce-ku-ce mai zafi a jihar, musamman ganin cewa wata kotun Benin ta hana a yi hakan
- Sai dai gwamnatin Edo ta ce ta nada ciyamomin riko domin cike gibin shugabanci bayan majalisar jihar ta dakatar da masu mulkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Edo - Duk da matsayin gwamnatin tarayya kan 'yancin kan kananan hukumomi, Gwamnan Edo Monday Okpebholo ya rantsar da ciyamomin riko na kananan hukumomi 18.
Wannan matakin ya haifar da rudani yayin da aka hana ciyamomin gudanar da ayyuka a ofisoshin kananan hukumomi, inda aka tura masu 'yan dabar siyasa.
Gwamnan Edo ya rantsar da ciyamomin riko
Rahoton Arise News ya nuna cewa majalisar Edo ta dakatar da ciyamomin jihar kan rashin biyayya bayan wata wasika da gwamnan ya aike masu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwana guda kacal bayan haka, Antoni Janar na tarayya Lateef Fagbemi, ya jaddadawa Gwamna Okpebholo matsayin kotun koli kan ‘yancin kananan hukumomi.
Fagbemi ya ce gwamnoni da 'yan majalisa ba su da iko na dakatar da shugabannin kananan hukumomi; yana mai cewa "wannan iko yana hannun kansilolin kananan hukumomi".
Gwamnatin Edo ta yi wa Ministan shari'a martani
Sai dai gwamnatin Edo ta yi martani da cewa ta rantsar da ciyamomin riko ne domin cike gibin shugabancin da aka samu sakamakon korar ciyamomin da majalisa ta yi.
An samu labarin cewa a ranar Litinin Okpebholo ya rantsar da ciyamomin kananan hukumomi 18, duk da hukuncin da wata kotu ta yanke a makon jiya.
Kotun Benin karkashin Mai Shari’a Efe Ikponmwonba ta umurci majalisar dokokin jihar da ka da ta kori ciyamomin har sai an kammala sauraron karar da ke gabanta.
Gwamnan Edo ya bijirewa umarnin kotu
An ce ciyamomin sun gaza sanya majalisar dokokin jihar a cikin jerin wadadanta take kara, lamarin da ya ba gwamnatin jihar damar aiwatar da sabon matakin.
Wata majiyar gwamnati da ta tabbatar da lamarin, ta ce gwamnatin jihar ta umurci ciyamomin da su mika shugabanci ga jagororin majalisar kananan hukumominsu.
Wannan lamari ya haifar da rudani a fadin jihar, musamman ganin cewa an yi hakan ba tare da la'akari da matsayin kotun kan batun ba.
EFCC ta gayyaci ciyamomin Edo 18
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar EFCC ta gayyaci ciyamomi 18 da aka dakatar da su a jihar Edo kan zargin sama da fadi da kudin kananan hukumomi.
A cikin wasiku daban daban da aka aikawa kowane ciyaman, EFCC ta bukaci shugabannin da su je ofishinta tare da wasu takardu a ranaku biyu da ta ware masu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng