'Ku Koyi Rayuwa a Haka': Tinubu Ya ba yan Najeriya Satar Amsa kan Tsadar Wutar Lantarki

'Ku Koyi Rayuwa a Haka': Tinubu Ya ba yan Najeriya Satar Amsa kan Tsadar Wutar Lantarki

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su koyi yadda za su rage amfani da makamashi domin daina kukan tsada
  • Bola Tinubu ya bayyana cewa ba ya goyon bayan kara farashi, amma gwamnati za ta yi kokarin samar da kayayyaki masu araha
  • Farashin mai da wutar lantarki sun yi tashin gwauron zabi tun bayan cire tallafin man fetur, wanda ya janyo suka daga al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi magana kan yadda yan kasa za su rage amfani da wutar lantarki.

Tinubu ya shawarci ‘yan Najeriya su koyi yadda za su kula da amfani da wutar lantarki don rage yawan kudin wuta.

Tinubu ya ba yan Najeriya shawara kan amfani da wutar lantarki
Bola Tinubu ya shawarci yan kasa kan rage amfani da wutar lantarki. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Rayuwa ta yi tsada bayan cire tallafin mai

Tinubu ya fadi haka ne yayin hira da yan jaridu wanda hadiminsa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan

Radadin cire tallafi: Tinubu ya fadi yadda abokinsa ya gagara rike manyan motoci 5

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin kudin wuta tare da matsin tattalin arziki ya haifar da koke-koke daga ‘yan Najeriya da ke fama da tsadar rayuwa da karancin kudin shiga.

A watan Afrilu 2024, hukumar kula da wutar lantarki ta kara kudin wuta daga N66 zuwa N225 ga abokan ciniki da ke sahun farko watau 'Band A'.

Tun bayan rantsar da shi a watan Mayu 2023, an samu hauhawar farashin makamashi sakamakon cire tallafin mai da karin kudin wutar lantarki.

Wutar lantarki: Tinubu ya ba yan Najeriya shawara

Shugaban Najeriya ya ce ba laifi ba ne domin yan kasa sun koyi yadda za su samar wa kansu sauki saboda tsadar wutar lantarki.

Ya ce ba ya goyon bayan tsadar farashin wutar lantarki inda ya yi alkawarin samar da kayayyaki masu sauki.

"Ba laifi ba ne koyon yadda ake sarrafa kudin wuta, kamar kashe fitilu idan ba a bukata."

- Bola Tinubu

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Tinubu ya fadi shirin gwamnatinsa a kan rage tsadar kayayyaki

Tinubu ya magantu kan cire tallafin mai

Kun ji cewa a ranar Litinin shugaba Bola Tinubu ya ce bai yi nadama kan cire tallafin man fetur a watan Mayu 2023 da ya yi ba.

Tinubu ya bayyana cewa cire tallafin ya kawo gasa a bangaren man fetur, inda ya ce farashin ya fara raguwa a halin yanzu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.