Kwana Ya Kare: Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon AIG Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Allah ya yi wa tsohon mataimakin sufetan ƴan sanda (AIG), Emmanuel Adebola Longe rasuwa ranar Lahadi da ta gabata
- Shugaban kungiyar lauyoyi reshen Oyo, Ibrahim Lawal ya tabbatar da rasuwar tsohon AIG a wata sanarwa ranar Litinin
- Marigayin dai ya yi abubuwan da zai wahala a manta da shi a rundunar ƴan sandan Najeriya, ya shafe sama da shekara 30 a bakin aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mataimakin Sufeto-Janar na ‘yan sandan Najeriya (AIG), Emmanuel Adebola Longe (mai ritaya) ya riga mu gidan gaskiya.
Tsohon AIG na rundunar ƴan sandan ya rasu ne a ƙarshen makon da ya gabata, ranar Lahadi, 22 ga watan Disamba, 2024.
Najeriya ta yi rashin tsohon AIG
Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA) reshen Ibadan, Ibrahim Lawal ya tabbatar da rasuwar a wata tattaunawa da Tribune Online ta wayar tarho.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun kafin haka kuma shugaban NBA ya fitar da sanarwar a hukumance don tabbatar da rasuwar Adebola Longe.
Sanarwar ta ce:
"Mun samu labarin rasuwar Fasto Bola Longe, mataimakin Sufeta-Janar na ƴan sanda mai ritaya, abokin hulɗar cambar Afe Babalola & co, ya rasu ne jiya (Lahadi)."
"Ƙungiyar lauyoyi na miƙa ta'aziyya ga iyalan marigayin da abokan aikinsa, muna addu'ar Allah ya jiƙansa."
Taƙaitaccen bayani game da tsohon AIG
Longe shi ne ɗan sandan da ya jagoranci tarwatsa daya daga cikin manya-manyan barayin layin dogo a yankin Arewa ta Tsakiyar Najeriya a shekarar 2021.
Ya yi ritaya daga aikin rundunar ‘yan sandan Najeriya bayan shekaru 33 da watanni takwas yana yiwa kasarsa hidima.
Bola Longe ya yi ritaya daga mukamin mataimakin babban sufeton ‘yan sanda, watau AIG mai kula da ayyukan tarayya a hedikwatar rundunar da ke Abuja.
Marigayin tsohon dalibi ne a jami’ar Ibadan (UI) da ke jihar Oyo da kuma Jami’ar Legas.
Tsohon gwamna a Najeriya ya kwanta dama
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom a zamanin mulkin soji, Godwin Osagie Abbe ya kwanta dama.
An ruwaito cewa marigayin, wanda ya taɓa rike kujerar minista, ya mutu ne bayan fama da jinya ranar Asabar da ta gabata.
Asali: Legit.ng