"50 Sun Yi Yawa": Bola Tinubu Ya Yi Bayani kan Yiwuwar Ya Sake Korar Wasu Ministoci

"50 Sun Yi Yawa": Bola Tinubu Ya Yi Bayani kan Yiwuwar Ya Sake Korar Wasu Ministoci

  • Shugaaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya musanta batun rage yawan ministoci a gwamnatinsa, ya ce kowane da aikin da ya rataya a wuyansa
  • Majalisar zartarwa ta gwamnatin Tinubu mai kimanin ministoci 50 ita mafi girma da aka taɓa yi a Najeriya
  • Da yake maida martani ga masu sukar yawan muƙarrabansa, Bola Tinubu ya ce dukkansu akwai aikin da ya ba su kuma suna yin yadda ya dace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

State House, Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi fatali da raɗe-raɗin da ake cewa da yiwuwar ya rage wasu ministoci a gwamnatinsa.

Majalisar zartaswar Bola Tinubu mai kimanin ministoci 50 ita ce mafi girma da aka taɓa yi a tarihin Najeriya.

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Bola Tinubu ya kore yiwuwar rage yawan ministoci a gwamnatinsa Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Daily Trust ta ce hakan ya sa mutane dama suka fara sukar gwamnatin Tinubu musamman ƴan adawa, suna cewa wasu ministocin zaman dumama kujera kawai suke yi.

Kara karanta wannan

"Ba abin da za a fasa," Bola Tinubu ya sake magana mai ɗumi kan kudirin haraji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ba zai rage yawan ministoci ba

Da yake martani kan lamarin, Shugaba Tinubu ya ce dukkan ministocin da ake gani ya naɗa su ne da wata manufa, musamman manufar hidima ga Najeriya.

Ya yi wannan furucin ne a zaman tattauwa da ƴan jarida karon farko wanda gidan talabijin na ƙasa NTA ya watsa kai tsaye.

"Ban shirya rage yawan ministoci na ba, na farko dai na san bukatar da ta sa na naɗa su, ba zai yiwu ka ba wani aikin da ka san ba zai iya ba."
"Dole ne mu yi aiki mai nagarta da inganci, Najeriya babbar ƙasa ce, saboda da haka ina gani zai fi dacewa mu maida hankali kan yin ayyukan da suka dace."

- Bola Tinubu.

Shugaba Tinubu ya ce ministoci da aiki

Dangane da zargin akwai ƴan dumama kujera, Tinubu ya kalubalanci ƴan jaridar da ke hira da shi su faɗi sunayen ministocin da suka gaza yin aikin da ke kansu.

Kara karanta wannan

Yadda gwamnatin Tinubu ta shirya rabon tallafin N25,000 ga magidanta miliyan 15

Bugu da ƙari da aka tambayi ko duka ministocin ma ƙarawa gwamnatinsa ƙima a idon ƴan Najeriya, Tinubu ya ce, "Kwarai da gaske, ku nuna mun wanda ya gaza."

Bola Tinubu ya warewa su Buhari N27bn a 2025

Kun ji cewa Shugaba Tinubu ya ware kimanin Naira biliyan 27 domin yi wa tsofaffin shugabannin ƙasa da mataimakansu hidima.

Za a yi amfani da kudin ne wajen biyan hakkoki da kula da tsofaffin shugaɓan ƙasa da suka haɗa da Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan a 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262