Gwamnan Katsina Ya Cika Alkawari, Ya Sa Malaman Makaranta cikin Farin Ciki
- Ma'aikatan jihar Katsina sun nuna farin ciki da Gwamna Dikko Radda ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000
- A farkon watan nan Malam Dikko ya yi alkawarin aiwatar da dokar sabon albashin bayan cimma matsaya da ƴan kwadago
- Wani malamin firamare ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan ƙarin zai taimake su matuka a halin tsadar da ake ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Katsina - Ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina sun fara karɓan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a watan da muke ciki watau Disamba, 2024.
Tun farko dai Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya yi alkawarin fara biyan sabon albashin a watan Disamba bayan cimma matsaya da ƴan kwadago.
Hadimin gwamnan Katsina da ya yi murabus saboda zai nemi takarar ciyaman, Isah Miqdad ne ya tabbatar da fara biyan sabon albashin a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan Katsina ya cika alƙawarin da ya ɗauka
Ya ce Malam Dikko Radda ya cika alkawarin da ya ɗauka na fara biyan sabon albashin, inda ya ce malaman makaranta sun samu sama da N70,000.
Isah Miqdad ya ce:
"Kamar yadda Gwamna Dikko Radda ya yi alkawari, ya fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar Katsina."
Malaman makaranta sun yabawa gwamna
Wani malamin makarantar firamare, Bashir Yusuf ya tabbatar da fara biyan sabon albashin ga wakilin Legit Hausa.
Ya ce gwamnatin Katsina ta biya albashin watan Disamba yau Litinin kuma an yi ƙari kamar yadda gwamna ya yi alƙawari.
Malam Bashir ya yabawa gwamnatin Katsina bisa cika alƙawarin da ta ɗauka, yana mai cewa ƙarin zai ragewa ma'aikata raɗaɗin kuncin da suka shiga.
"Eh an fara biyan sabon mafi karancin albashi, ni kaina na ga ni kuma tsakani da Allah ma'aikata suna cikin farin ciki.
"Zaka ga malamin makaranta da ke ɗaukar N39,000 yanzu ya koma kusan N80,000, ka ga za a samu sauki. A wannan ɓangaren dai muna yabawa mai girma gwamna."
Gwamna Eno ya gindaya sharaɗin ƙara albashi
Kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom ya gindaya sharaɗi ga ma'aikata kafin fara tura masu N80,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.
Fasto Umo Eno ya ce ba zai fara biyan sabon albashin ba har sai gwamnatinsa na gama tantance ma'aikata a Akwa Ibom.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng