Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi ga 'Yan Najeriya, Ya Sanya Lokacin Hirar Farko
- Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tattauna da ƴan jarida a karon farko tun bayan hawansa kan madafun ikon ƙasar nan
- Mai taimakawa shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa za a yi tattaunawar ne a daren ranar Litinin
- Onanuga ya ƙara da cewa za a watsa tattaunawar ne a tashar talabijin ta NTA da gidan rediyon FRCN da misalin ƙarfe 9:00 na dare
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tattauna da ƴan jarida a karon farko.
Shugaba Tinubu zai yi tattaunawar ne wacce ita ce ta farko tun bayan hawansa mulki a ranar Litinin, 23 ga watan Disamban 2024.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a watsa tattaunawar ne a gidan talabijin na Najeriya (NTA) da kuma gidan rediyon tarayyar Najeriya (FRCN).
Bayo Onanuga ya ce za a watsa tattaunawar ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren yau Litinin.
"Za a watsa tattaunawar farko da ƴan jarida tare da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, da ƙarfe 9:00 na dare a ranar Litinin, 23 ga watan Disamba, a tashar NTA da gidan rediyon FRCN."
"Ana buƙatar tashoshin talabijin da gidajen rediyo su kama domin tattaunawar."
- Bayo Onanuga
Gwamnati sun raba tiriliyoyi a Najeriya
A baya rahoto ya zo cewa Naira tiriliyan 3.14 ya shigo cikin asusun gwamnatin tarayya kuma an raba Naira tiriliyan 1.7 daga asusun FAAC a Nuwamba.
Gwamnatin tarayya ta samu N580bn, an raba N549bn tsakanin gwamnonin jihohi 36 sannan shugabannin kananan hukumomin sun samu N402.55bn.
Asali: Legit.ng