Ana Fatan Kara Samun Saukin Fetur bayan an Sake Kira ga Gwamnati

Ana Fatan Kara Samun Saukin Fetur bayan an Sake Kira ga Gwamnati

  • Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da kungiyoyin fararen hula sun nuna rashin gamsuwa da rage farashin litar fetur zuwa N935
  • Hakan na zuwa ne yayin da matatar Dangote da NNPCL suka rage farashin mai amma NLC ta ce har yanzu akwai bukatar karin ragi
  • Kungiyoyin sun bukaci gwamnati ta sake duba farashin domin rage shi tare da bayyana gaskiyar yadda take tace mai a matatar Fatakwal

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) da wasu kungiyoyin fararen hula sun yi kira da a sake rage farashin fetur, bayan sanarwar da aka yi cewa za a sayar da lita N935.

Korafin ya biyo bayan matsayar da matatar Dangote da MRS suka cinma ne kan rage farashin fetur wanda NNPCL ma ya rage farashin daga baya.

Kara karanta wannan

Hauhawar farashi: Tinubu ya fadi shirin gwamnatinsa a kan rage tsadar kayayyaki

NLC|Fetur
NLC ta bukaci rage farashin fetur. Nigeria Labour Congress|Kola Sulaimon
Asali: UGC

Rahoton Punch ya tabbatar cewa wani jigo a NLC, Chris Onyeka, ya bayyana cewa sabon farashin bai yi daidai da gaskiyar abin da ya kamata a rika saye a Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NLC ta bukaci rage farashin man fetur

Wani jagora a kungiyar NLC, Chris Onyeka, ya nuna cewa sabon farashin fetur bai yi wa ’yan Najeriya daidai ba, inda ya ce:

"Ba za mu yi farin ciki da farashin lita a kan N935 ba. Wannan farashin bai dace da yanayinmu ba."

Chris Onyeka ya kara da cewa tsarin farashin da ake amfani da shi an gina shi ne a kan yadda ake shigo da fetur daga waje alhali a Najeriya ake tace mai din.

Ya kuma yi kira da cewa dole ne gwamnati ta bayyana yawan kudin da ake kashewa wajen tace fetur a Najeriya, domin hakan ne zai sa a gano yadda farashin ya kamata ya kasance.

Kara karanta wannan

N965: Kamfanin mai na NNPCL ya sauke farashin fetur

Kungiyoyi sun bukari rage kudin mai

Shugaban Cibiyar Accountability and Open Leadership, Debo Adeniran, ya ce farashin litar fetur a N935 ya yi tsada sosai.

Debo Adeniran ya ce ya kamata gwamnati ta bayar da cikakken bayanin yadda ake fitar da farashin.

A cewarsa, akwai kasashe irin Libya da ke sayar da fetur kamar kyauta ga ’yan kasa, kuma ya kamata Najeriya ta dauki wannanar hanyar domin rage radadi ga talakawa.

Za a yi bincike a matatar Fatakwal

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin fararen hula za su je binciken kwakof a matatar Fatakwal domin duba halin da take ciki.

Kungiyoyin sun bayyana cewa za su hada tawaga mai mutane 50 domin binciken kuma za su fitar da rahoto ga 'yan kasa kan abin da suka gani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng