Gwamna a Arewa Ya Kirkiro Sababbin Masarautu da Sarakuna 7 Masu Daraja
- Gwamna Ahmadu Fintiri na jihar Adamawa ya kirkiro sababbin masarautu masu daraja ta biyu da masu daraja ta uku guda 7
- Ahmadu Fintiri ya bayyana cewa ya yi haka ne ba don kara faɗaɗa ayyukan sarakuna waɗanda ke ba da gudummuwa ta fannoni daban-daban
- Wasu dai na ganin gwamnan ya kirkiro sababbin masarautun ne domin rage karfin ikon Mai martaba Lamidon Adamawa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri ya kirkiro sababbin masarautu da sarakuna bakwai a faɗin jihar Adamawa.
Gwamna Fintiri ya sanar da haka ne a wani jawabin kai tsaye da ya yi ga al'ummar jihar Adamawa ranar Litinin, 23 ga watan Disambar, 2024.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Ahmadu Fintiri ya ce ya ɗauki wannan matakin domin inganta ayyukan sarakuna wajen samar da zaman lafiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fintiri ya kirkiro masarautu 7
Ya lissafo sababbin masarautun da suka haɗa da masarautar Huba a Hong, masarautar Madagali mai hedikwata a Gulak, da masarautar Michika mai hedikwata a Michika.
Sauran sun ƙunshi masarautar Fufore mai hedikwata a Fufore, masarautar Gombi mai hedikwata a Gombi, masarautar Yungur mai hedikwata a Dumne, da masarautar Maiha mai hedikwata a Maiha.
A cewar gwamnan, za a naɗa sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Huba, Madagali, Michika, da masarautar Fufore
Sai kuma masarautun Gombi, Yungur da kuma Maiha da Gwamna Fintiri ya ce an ba su matsayin darajata ta uku.
Dalilin kirkiro sababbin masarautu 7
"Manufar kirkiro waɗanna sababbin masarautun ita ce ƙara inganta ayyukan sarakuna a fannin samar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban Adamawa," in ji shi.
Fintiri ya ƙara da cewa ana kuma sa ran matakin zai samar da karin cibiyoyin warware sabani, inganta harkokin mulki da kuma karfafa hadin kan al’umma.
Za a rage karfin ikon lamidon Adamawa?
A wani labarin, kun ji cewa
Majalisar Dokokin Adamawa ta musanta wasu raɗe-raɗin da ke cewa sabuwar dokar masarauta za ta rage ikon Lamidon Adamawa.Ana dai yaɗa jita-jitar cewa sabuwar dokar da Majalisar ke shirin amincewa da ita na shirin sauke Lamidon Adamawa daga matsayin shugaban sarakunan Adamawa.
Asali: Legit.ng