Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Goyi bayan Kudirin Harajin Tinubu

Shugabannin Kiristocin Arewa Sun Goyi bayan Kudirin Harajin Tinubu

  • Kungiyar Kiristocin Arewa ta yi watsi da zargin cewa kudirin harajin shugaba Bola Tinubu yana adawa da yankin Arewa
  • CHAIN ta bayyana haka ne yayin gudanar da wani taron tattaunawa a jihar Kaduna kan batun haraji da tasirinsa ga al’umma
  • Shugabannin kungiyar sun yi kira da a rungumi gaskiya tare da bayar da gudunmawa wajen gina kasa mai inganci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Shugabannin Kiristoci a Arewa sun bayyana goyon bayansu ga kudirin harajin shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka gabatar wa Majalisar Tarayya

Sun cimma matsayar ne bayan taron tattaunawa da kungiyar Kiristocin Arewa ta CHAIN ta shirya a Kaduna karkashin shugabannin Kiristoci na jihohi 19 da Abuja.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaban majalisa ya yi zazzaga, ya tona yadda aka rugurguza Arewa

Tinubu
Shugabannin Kiristoci sun goyi bayan kudirn harajin Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Leadership ta wallafa cewa an tattauna batun tare da masana kan dokokin haraji yayin da taron ya gudana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin Kiristoci vs harajin Tinubu

Channel Television ya rahoto cewa Manyan shugabannin Kiristoci daga Arewa ciki har da tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Yakubu Dogara sun hallara taron.

Masana kamar Farfesa Seth Akutson da kuma lauya Samuel Atung, sun bayyana amfanin gyaran harajin ga ci gaban kasa.

Sun bayyana cewa haraji abu ne da ke kunshe cikin addinin Kirista, inda suka ambaci Yesu ya koyar da mabiyansa su biya haraji ga mahukunta.

Matsayar taron Kiristoci a Kaduna

Daga cikin abunuwan da aka cimma bayan taron akwai cewa:

1. Al’ummar Kiristoci su kasance masu shiga cikin harkokin gwamnati da kula da al’amuran da suka shafi rayuwar ‘yan kasa.

2. Jama’a su nisanci kalaman batanci da rarrabuwa da ka iya kawo baraka ga hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

3. Kiristoci su bayar da shawara ga wakilansu a majalisun jiha da na tarayya domin tabbatar da cewa an magance duk wasu sabani kafin a zartar da kudirin.

4. Dukkan ‘yan kasa su kasance masu bayar da gudunmawa ga ci gaban kasa.

5. Shugabannin Arewa su jagoranci shirya ranar addu’a domin neman rahamar Allah kan matsalolin da suka hada da rashin tsaro, rashin ci gaba, da sauransu.

A karshe, shugabannin sun bayyana cewa zargin cewa kudirin yana adawa da Arewa ba shi da tushe.

Tinubu ya sake magana kan haraji

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake magana kan kudirin haraji inda ya ce zai taimaka ga kasa.

Shugaban kasar ya bayyana haka ne a jihar Ibadan inda ya ce bai kamata a rika ce-ce-ku-ce kan kudirin ba saboda amfanin da yake da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng