N965: Kamfanin mai na NNPCL ya sauke farashin fetur

N965: Kamfanin mai na NNPCL ya sauke farashin fetur

  • Rahotanni na nuni da cewa farashin litar man fetur ya sauka zuwa N965 a gidajen man Najeriya na NNPC a birnin tarayya Abuja
  • Hakan na zuwa ne yayin da matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur a Najeriya domin samun saukin bikin karshen shekara
  • An samu saukin farashin idan aka kwatanta da yadda ‘yan kasuwa masu zaman kansu ke sayar da litar fetur tsakanin N1,030 zuwa N1,070

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Farashin litar man fetur ya sauka zuwa N965 a gidajen mai na kamfanin NNPC da ke Abuja, babban birnin tarayya.

Binciken da aka gudanar a yau Litinin ya tabbatar da cewa NNPC ya rage farashin man fetur a dukkan gidajen man sa da ke birnin, abin da ya sanya direbobi farin ciki.

Kara karanta wannan

Wike ya shirya tatsar N0bn daga masu filaye a Abuja, an gindaya wa'adin biyan kudi

NNPCL
NNPCL ya sauke farashin mai a Abuja. Hoto: NNPC Limited
Asali: Facebook

Punch ta wallafa cewa wannan saukar farashi shi ne karo na biyu a cikin kasa da makonni biyu, bayan da aka sayar da shi N1,060 a farkon watan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu layuka a gidajen man NNPCL

A gidajen mai na NNPCL da ke Wuse Zone 4 da kuma kan titin Olusegun Obasanjo da ke yankin Central Area, an sayar da man a farashin N965, lamarin da ya janyo dogayen layuka.

Wani direba da ya tabbatar da saukar farashin ya jinjinawa NNPC amma ya yi kira da a tabbatar da daidaituwar farashin a duk gidajen mai.

Ga abin da ya ce:

“NNPC sun rage farashin zuwa N965. Na saya da safe amma layin ya yi tsawo sosai saboda wasu gidajen mai ba su daidaita farashin ba”

Farashin ‘yan kasuwa masu zaman kansu

A gefe guda, masu kasuwancin mai na ‘yan kasuwa masu zaman kansu da manyan dillalai suna sayar da man fetur tsakanin N1,030 zuwa N1,070 a Abuja.

Kara karanta wannan

IPMAN da matatar Dangote sun shiga yarjejeniyar rage farashin fetur zuwa N935

A ranar Lahadi, shugaban kungiyar dillalan man fetur ta Najeriya (IPMAN), Maigandi Garima, ya bayyana cewa farashin litar fetur zai kasance N935 daga ranar Litinin.

A halin yanzu dai 'yan Najeriya na tsammanin cigaba da samun saukin farashin man fetur a jihohi musamman a gidajen man NNPCL.

Za a kai ziyarar bincike matatar Fatakwal

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyoyin fararen hula sun za su ziyarci matatar man Najeriya da ke Fatakwal domin gano halin da ta ke ciki.

Rahotanni sun nuna cewa kimanin mutane 50 aka nada domin zuwa matatar kuma za su fitar da rahoto na musamman bayan kammala ziyarar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng