Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'adda a Wajen da Suke Tsafi, An Kashe Miyagu da Dama

Sojoji Sun Ritsa 'Yan Ta'adda a Wajen da Suke Tsafi, An Kashe Miyagu da Dama

  • Rundunar Operation UDO KA ta Kudu Maso Gabas ta kashe mambobin kungiyar 'yan ta'addar IPOB yayin farmaki da ta kai musu
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa rundunar ta kama masu garkuwa da mutane 3 tare da kwace makamai da kayayyaki a wajensu
  • Rundunar sojin Najeriya ta samu nasarar wargaza wani waje da 'yan ta'addar ke amfani da shi wajen yin tsafi a mafakar wani shugabansu

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - Rundunar sojojin haɗin gwiwa ta Operation UDO KA ta Kudu Maso Gabas ta bayyana cewa ta kashe 'yan ta'addar kungiyar IPOB da dama.

Haka zalika, rundunar ta cafke masu garkuwa da mutane uku a wani aikin sintiri a yankin Kudu Maso Gabas domin tabbatar da zaman lafiya a lokacin bikin karshen shekara.

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

Sojoji
Sojoji sun kashe 'yan ta'addar IPOB. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Getty Images

Punch ta wallafa cewa kakakin rundunar, Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Enugu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laftanar Kanal Jonah Unuakhalu ya jaddada cewa tsaron yankin abu ne da suka ba muhimmanci saboda haka za su yi maganin duk wani mai tayar da kayar baya.

Sojoji sun farmaki masu garkuwa a Enugu

A ranar 21 ga Disamba, dakarun rundunar sun gudanar da kwanton-bauna a kan hanyar Amouka-Umouka da ke karamar hukumar Udi a jihar Enugu.

A lokacin farmakin, an kashe daya daga cikin masu garkuwa da mutanen yayin da sauran suka tsere da raunukan harsasai.

The Guardian ta wallafa cewa sojojin sun kwace bindiga AK-47 daya, alburusai 17, wayoyi biyu, da wasu kayayyaki masu mahimmanci.

An lalata kayan tsafe-tsafen IPOB

A ranar 16 ga Disamba, dakarun rundunar sojin Najeriya sun gudanar da farmaki a yankin Mbosi da Isseke na karamar hukumar Ihiala a jihar Anambra.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun cafke 'yan tawayen kasar waje da suka shigo jihar Arewa

A farmakin, an kashe mambobin IPOB uku tare da lalata wani gidan shugaban kungiyar da kuma wani wajen tsafe-tsafe da suke amfani da shi domin samun kariya.

An kwace bindigu AK-47 guda daya, bindigu guda uku na gida, da kayan fashewa guda biyar, da sauran kayayyaki masu hatsari daga hannun ‘yan kungiyar.

An kama mai taimakon Bello Turji

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Najeriya ta yi nasarar cafke wasu mutane biyar da ke da alaka da Bello Turji.

A yau Litinin aka gurfanar da mutanen da ake zargin a kotun tarayya a Abuja inda aka zarge su da taimakawa dan ta'adda, Bello Turji da makamai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng