Matawalle Ya Yi Maraba da Dawo da Hakar Ma'adanai a Zamfara, Ya Fadi Amfanin Hakan

Matawalle Ya Yi Maraba da Dawo da Hakar Ma'adanai a Zamfara, Ya Fadi Amfanin Hakan

  • Bello Matawalle ya yi maraba da matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na ɗage haramcin haƙo ma'adanai a Zamfara
  • Ƙaramin ministan tsaron ya bayyana cewa dawo da haƙar ma'adanan zai bunƙasa tattalin arziƙin jihar da samar da ayyukan yi
  • Matawalle ya kuma nuna masu zuba hannun jari za su shigo cikin jihar sakamakon ɗage haramcin da gwamnatin tarayya ta yi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya yi magana kan ɗage haramcin haƙar ma'adanai a Zamfara.

Bello Matawalle ya bayyana cewa matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka na dawo da haƙar ma’adanai a Zamfara zai kawo masu zuba jari da kuma bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Matawalle ya yaba da dawonda hakar ma'adanai a Zamfara
Matawalle ya ce dawo da hakar ma'adanai a Zamfara zai bunkasa tattalin arziki Hoto: @BelloMatawalle1
Asali: Twitter

Matawalle ya bayyana haka ne a yammacin ranar Lahadi, yayin da yake zantawa da manema labarai a Gusau babban birnin jihar Zamfara, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dage haramcin hakar ma'adanai a Zamfara, ta fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jihar Zamfara ta yi asara a baya

Bello Matawalle ya bayyana cewa tun bayan hana ayyukan haƙar ma’adanai a lokacin gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari saboda rashin tsaro, jihar ta tafka ɗimbin asara, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Ya bayyana jihar Zamfara a matsayin matattarar samar da ma’adanai, ya jaddada cewa ƴan ƙasashen waje da dama sun nuna sha’awar saka hannun jari musamman a ɓangaren lithium.

"Shugaban ƙasa na wancan lokacin (Buhari) ya sanya dokar hana haƙar ma’adanai da hana zirga-zirgar jiragen sama, amma idan ka duba abin da muke asara a jihar yana da yawa domin Zamfara matattara ce mai ɗimbin arziƙin ma’adanai."

- Bello Matawalle

Matawalle ya faɗi amfanin dawo da haƙar ma'adanai

A cewarsa, ɗage haramcin zai taimaka wajen jawo masu zuba jari a ciki da wajen ƙasar nan zuwa Zamfara.

Matawalle ya kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu ya bayar da umarnin cewa duk wani mai son zuba jari, zai sarrafa ma’adanan ne a jihar domin samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziƙi.

Kara karanta wannan

Ib rahimShekarau ya ba PDP lakanin karbar mulki a hannun APC a 2027

Matawalle ya yi magana kan ƴan Lakurawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙaramin ministan tsaro ya musanta cewa akwai ƴan ta'addan Lakurawa a Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.

Matawalle ya bayyana cewa babu wani yanki na Najeriya da ke da ƴan ta'addan na Lakurawa domin sojoji sun fatattake su zuwa ƙasarsu ta Mali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng