Gaskiya Ta Fito kan Zargin Sayar da Jiragen Najeriya ga Iran ba da Sanin Gwamnati ba
- Kamfanin Azman Air ya musanta zargin sayar da jirgin sama ga kasar Iran, yana mai cewa labarin kanzon kurege ne
- Rahotannani sun nuna cewa kamfanin ya ce jirginsa ya tafi Iran ne domin yin gyaran da ake bukata lokaci bayan lokaci
- Kamfanin Azman Air ya ce yana shirin daukar matakin doka kan masu yada labarin cewa ya sayar da jiragensa ga Iran
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Kamfanin Azman Air ya karyata zargin cewa ya sayar da jirgi ga Iran, yana mai cewa zargi ne da babu gaskiya a cikinsa.
Manajan kamfanin, Muhammad AbdulManaf, ya ce jirgin ya tafi Iran ne kawai domin wani gyara na musamman kamar yadda hukumar NCAA ta tanada.
Vanguard ta wallafa cewa AbdulManaf ya bayyana cewa kamfanin zai dauki mataki a kan sharri da aka masa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abin da ya kai jirgin Azman zuwa Iran
Azman Air ya ce tafiye-tafiyen jirginsa zuwa Iran ba wani abu ba ne illa na gyara na C-Check wanda ake bukata bayan kowane watanni 18.
AbdulManaf ya ce ya ji mamakin jin labarin cewa sun boye tafiyar jirgi zuwa Iran inda ya ce jirgi ba abu ne da za a iya boye tafiyarsa ba.
Ya kara da cewa akwai ka'ida daga NCAA kan sayarwa ko cire rajistar jirgi, kuma Azman Air ba ta aikawa NCAA wani takarda ba kan batun ba.
Zargin kashe na'urar jirgi a kasar Iran
Daily Trust ta wallafa cewa daga cikin batutuwan da ake bincike akwai zargin kashe wata na'ura ta musamman a lokacin da jirgin Azman ya isa Iran.
Kamfanin Azman ya bayyana cewa ya rubuta wa hukumar sufurin jiragen sama ta Iran domin neman karin bayani kan lamarin.
Yarjejeniyar tattalin arziki a kasashen D8
Kamfanin Azman Air ya kuma musanta sanin wata takaddama ko takunkumi tsakanin Najeriya da Iran.
Ya bayyana cewa akwai yarjejeniyar tattali tsakanin kasashen D8, wanda ya hada da Najeriya, Iran, da wasu kasashe, wacce ke bai wa kasashen damar yin cinikin kayayyaki.
Alhaji AbdulManaf ya jaddada cewa kamfanin zai ci gaba da kare martabar sa ta hanyar bin doka da oda.
Za a gina filin jirgin sama a Zamfara
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Zamfara karkashin Dauda Lawal Dare ta bayyana shirin gina katafaren filin jirgin sama.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa samar da filin jirgin saman na da muhimmanci wajen gayyato masu zuba jari daga ketare.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng