Gwamnati Ta Yi Martani kan Zargin Jawo Mutuwar 'Yan Kasa wajen Karbar Tallafin Abinci

Gwamnati Ta Yi Martani kan Zargin Jawo Mutuwar 'Yan Kasa wajen Karbar Tallafin Abinci

  • Gwamnatin tarayya ta karyata cewa manufofin da gwamnatin Bola Tinubu ta zo da su sun taka rawa wajen jawo yunwa
  • Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a. Mohammed Idris ne ya bayyana haka ya ce bai dace rika siyasantar da batun ba
  • Ya shawarci mutanen da ke da shirin raba tallafi ga mutanen Najeriya da su tabbata sun tuntubi hukumomi kafin rabon

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Gwamnatin Tarayya ta fusata da yadda wadansu mutanen kasar nan da ‘yan adawa ke kokari dora alhakin mutuwar jama’a a kan gwamnatin tarayya.

Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris ya ce wadannan al’amura abin takaicin ne matuka, amma ba su da alaka da manufofin tattalin arziki na gwamnati.

Kara karanta wannan

"Mun samu nasara:" Sanata Ndume ya fadi amfanin watsi da kudirin harajin Tinubu

HMMohammedIdris
Gwamnati ta yi martani kan zargin gwamnati da jawo yunwa Hoto: @HMMohammedIdris
Asali: Twitter

Jaridar The Nation ta bayyana cewa an taba samun irin wadannan matsaloli a baya, saboda haka ba matsala ce da ta zo saboda gwamnatinsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnatin Tinubu ta ja kunnen ‘yan siyasa

Jaridar Thisday ta ruwaito gwamnatin tarayya ta ja kunnen ‘yan siyasa da su daina siyasantar da iftila’in da faru a jihohin kasar nan, inda jama’a da dama suka rasa rayukansu.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris ya ce;

“Ya kamata a fahimci cewa an taba samun irin wadannan munanan al’amura a baya, kafin wannan gwamnati ta zo. Don haka, duk wani yunkuri na danganta wadannan munanan abubuwa da sauye-sauyen shugaban kasa ba su da tushe kuma ba gaskiya ba ne.”

Gwamnati ta shawarci masu rabon tallafi

Gwamnatin Bola Tinubu ta yaba da kyakkyawan aniyar wasu daga cikin ‘yan kasar nan da ke kokarin bayar da tallafi ga masu karamin karfi.

Amma an yi gargadin yadda za a kawo sauki wajen samun turmutsutsu ta hanyar sanar da hukumomin da jami’an tsaro domin tseratar da rayukan jama’a.

Kara karanta wannan

Yunwa: PDP ta alakanta turmutsitsin da ya hallaka jama'a da manufofin Tinubu

Jam'iyyar PDP ta soki gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar adawa ta PDP ta dora alhakin turmutsutsin da ya kashe mutane da dama a jihohin Oyo, FCT da Anambra a kan talaucin da ta ce gwamnati ta jawo.

Jami'in hulda da jama'a na jam'iyyar na kasa, Debo Ologunagba ya fitar da sanarwar da ke nuna rashin jin dadin yadda gwamnati ta gaza samar da manufofin da za su kawo sauki ga jama'a.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.