Bukukuwan Kirsimeti: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranakun Hutu
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba da hutu domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekarar 2025 da za a shiga kwanan nan
- Ministan harkokin gida ya ayyana ranakun Laraba, 25 ga Disamba, Alhamis 26 ga Disamba da Laraba, 1 ga watan Janairu a matsayin ranakun hutu
- Olabunmi Tunji-Ojo ya kuma yi wa ƴan Najeriya murnar zagayowar lokacin bukukuwan inda ya buƙace su da su ci gaba da haɗa kawunansu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ta ayyana ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.
Gwamnatin ta ayyana ranar Laraba 25 ga Disamba, Alhamis 26 ga watan Disamba, 2024, da Laraba 1 ga Janairu, 2025 a matsayin ranakun hutu domin bukukuwan Kirsimeti, 'boxing day' da sabuwar shekara.
Babbar sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani, ta bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Litinin a Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta ba da hutun Kirsimeti
Ta bayyana cewa ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.
A cewarta, ministan ya yi fatan alheri ga ɗaukacin ƴan Najeriya, inda ya buƙace su da su yi amfani da lokacin bukukuwan domin yin la’akari da ƙimar soyayya, zaman lafiya da haɗin kai da wannan lokacin ke nunawa.
Dakta Olabunmi Tunji-Ojo ya jaddada muhimmancin bukukuwan a matsayin lokacin da ya kamata a inganta jituwa da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jama'a, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Ministan ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya da su ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai da ci gaban ƙasa.
Ya kuma ba ƴan kasar tabbacin ci gaba da aiwatar da ƙudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da zaman lafiya, tsaro da walwala a faɗin ƙasar nan.
Gwamnatin tarayya ta ɗage haramcin haƙar ma'adanai
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ɗage haramcin da aka sanya kan haƙar ma'adanai a jihar Zamfara da ke yankin Arewa maso Yamma.
Ministan ma'adanai, Dele Alake, wanda ya sanar da hakan ya ce an ɗauki matakin ne bayan an ƙara samun ingantar tsaro a jihar mai cike da ɗumbin albarkatun ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng