Yunwa: PDP Ta Alakanta Turmutsitsin da Ya Hallaka Jama'a da Manufofin Tinubu
- Jam'iyyar adawa ta PDP ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da bude kofar talauci da ta jawo yunwa a fadin kasar nan
- PDP ta na ganin wannan shi ne ya haddasa turereniyar da ta yi sanadiyyar mutuwar jama'a a wasu jihohin Najeriya
- A tsakanin mako guda, an samu mutuwar mutane a jihohin Oyo, Anambra da birnin Abuja yayin karbar tallafi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Jam’iyyar PDP ta ce turereniyar da aka samu a wasu sassan ƙasa kwanan nan tana “nuna tsananin wahala, talauci, da yunwa” da 'yan Najeriya ke fama da su.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, kakakin PDP, Debo Ologunagba, ya ce abin tausayi ne ganin 'yan Najeriya na mutuwa suna fafutukar neman abinci.
Jaridar The Cable ta wallafa cewa PDP ta dora alhakin haka a kan gazawar mulkin shugaba Bola Tinubu duk da albarkatun ƙasar da ake da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta zargi Bola Tinubu da rashin tausayi
Jaridar Nigerian Tribune ta wallafa cewa jam'iyyar hamayya ta PDP ta zargi gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da rashin tausayin talakawa.
Kakakin PDP, Debo Ologunagba ya ce;
“PDP ta bayyana turereniyar neman abinci da ke yawaita a ƙasar a matsayin shaida mai muni kan irin tsananin wahala, talauci, yunwa, yunƙurin rayuwa cikin ƙunci, da rashin fata da ke addabar ƙasarmu ƙarƙashin wannan gwamnatin Tinubu da ba ta da tausayi, cike da cin hanci, kuma ba ta da tsari."
Jam'iyyar PDP nemi gwamnatin Tinubu ta biya diyya
Babbar jam'iyyar adawa ta zargi gwamnatin Tinubu da rashin kula da darajar rayuwar ɗan Adam, tare da gaza iya ƙaddamar da shirye-shiryen tallafi don rage wa talakawa wahala. Sanarwar da PDP ta fitar ta ce;
“PDP tana kira ga 'yan Najeriya su ɗora alhakin waɗannan munanan abubuwan a kan gwamnatin Tinubu ta APC, wadda dole ne ta biya diyya kan abin da ya faru."
Jigon PDP ya yi ta'aziyya ga jihohi
A baya kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana takaicin mutuwar mutane da dama a jihohin Anambra da Oyo biyo bayan turmutsutsun karbar abinci.
Tsohon dan takarar a PDP ya bayyana cewa ba zai taba mantawa da wannan mummunan iftila'i ba, tare da shawartar masu shirya irin wadannan taruka a gaba domin kare rayukan jama'a.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng