Ibrahim Shekarau Ya ba PDP Lakanin Karbar Mulki a Hannun APC a 2027

Ibrahim Shekarau Ya ba PDP Lakanin Karbar Mulki a Hannun APC a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya fara taɓo batun zaɓen shekarar 2027 da ke tafe a ƙasar nan
  • Shekarau ya ba jam'iyyarsa ta PDP shawara kan hanyar da za ta bi domin sake dawowa kan madafun ikon ƙasar nan a 2027
  • Tsohon sanatan ya buƙaci PDP ta riƙe matasa hannu bibbiyu domin samun goyon bayansu a ƙoƙarin da take yi na raba APC da madafun iko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ba jam'iyyar PDP shawara kan zaɓen 2027 da ke tafe.

Ibrahim Shekarau ya buƙaci shugabannin PDP a dukkanin matakai da su riƙe matasan ƙasar nan, domin samun damar lashe zaɓen 2027.

Shekarau ya ba PDP shawara
Shekarau ya shawarci PDP kan zaben 2027 Hoto: Malam Ibrahim Shekarau
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shekarau ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a wajen taron ƙaddamar da kwamitin amintattu na ƙungiyar shugabannin matasan PDP na shiyya da jihohi a Abuja.

Kara karanta wannan

APC ta yi babban kamu, jiga jigan PDP sun koma jam'iyyar, sun fadi dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wace shawara Ibrahim Shekarau ya ba PDP?

Malam Shekarau ya bayyana cewa samun goyon matasa zai taimakawa jam’iyyar ta dawo domin ci gaba da riƙe madafun iko.

Ya kuma buƙaci matasa da su yi goyi bayan jam’iyyar PDP, a matsayin ta na zaɓi ɗaya tilo wanda zai fitar da Najeriya daga ƙalubalen da take fuskanta.

Tsohon gwamnan na Kano ya ce jam’iyyar PDP a tsawon shekaru 16 da ta yi tana mulki ta samar da ribar dimokuradiyya ga al’umma tare da kyautata rayuwa, kuma ya kamata a dawo da ita a shekarar 2027.

Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da, Hon. Enemona Anyebe (shugaban PDP na jihar Kogi), Dr. Joel E.B Adagadzu (sakataren tsare-tsare na shiyyar Arewa ta Tsakiya), Dr Yunana Iliya (tsohon jami'i na ƙasa) da dai sauransu.

Shekarau ya shawarci gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya ba da shawara ga gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

"PDP ta mutu murus," 'Yar Majalisar Tarayya ta ɗauki zafi bayan ta koma APC

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta sake lale kan yadda takd tafiyar da jagorancin ƴan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng