'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Bulla a Zamfara? Matawalle Ya Yi Bayani
- Ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle ya taɓo batun da ake yi kan cewa ƴan ta'addan Lakurawa sun ɓulla a jihar Zamfara
- Matawalle ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƴan ta'addan na Lakurawa a Zamfara har ma da jihar Kebbi da ke makwabtaka da ita
- Ƙaraminin ministan tsaron ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun fatattaki ƴan Lakurawa zuwa ƙasarsu ta Mali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Zamfara - Ƙaramin ministan tsaro, Bello Mattawalle ya yi magana kan batun ɓullar ƴan ta'addan Lakurawa a jihar Zamfara.
Matawalle ya ƙaryata iƙirarin da ake na cewa akwai ƴan ta'addan Lakurawa a jihar Zamfara.
Matawalle ya ce sojoji sun kori ƴan Lakurawa
Jaridar The Punch ta rahoto cewa Matawalle ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidansa da ke Gusau a daren ranar Lahadi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Matawalle ya ce ba gaskiya ba ne cewa ƴan ta'addan Lakurawa sun kasance a jihar.
Idan za a iya tunawa, kwamishinan ƴan sandan jihar Zamfara, Mohammed Shehu Dalijan, ya ce ƴan Lakurawa ne ke da alhakin dasa bama-baman da suka hallaka wasu mutane a jihar a kwanakin baya.
Matawalle ya bayyana cewa ƴan Lakurawa sun fito ne daga Jamhuriyar Mali kuma sojoji sun tilasta musu komawa ƙasarsu.
Matawalle ya musanta ɓullar ƴan Lakurawa a Zamfara
Ya kuma jaddada cewa ba su ma a jihar Kebbi kamar yadda kafafen yaɗa labarai suka ruwaito a baya.
A cewar Matawalle, sojoji sun fafata da su da kuma tilasta musu komawa ƙasarsu.
"Ina so na bayyana cewa, ba mu da ƴan Lakurawa a kowane yanki na ƙasar nan, ba ma a jihar Zamfara ko Kebbi ba."
Matawalle ya faɗi saƙon Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa.ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana saƙon da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ba da kan matsalar rashin tsaro.
Matawalle ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya umarci sojojinda su kawo ƙarshen ta'addancin da ƴan bindiga ke yi a cikin shekarar 2025 da ake tunkara.
Asali: Legit.ng