Kirsimeti: Buhari Ya Kadu da Iftila'in da Ya Faru, Ya Tura Sako ga Wike da Sauran Yan Najeriya
- Tsohon Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajanta wa Bola Tinubu kan turmutsitsin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane a jihohin Najeriya
- Buhari ya aika ta'aziyya ga gwamna Seyi Makinde da Chukwuma Soludo da Minista Nyesom Wike, tare da addu'ar samun sauki ga wadanda suka ji rauni
- Ya taya 'yan Najeriya murnar Kirsimeti da sabuwar shekara, yana rokon Allah ya kawo zaman lafiya da ci gaba mai dorewa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya jajanta kan rasa rayuka da aka yi a jihar Anambra da Oyo da birnin Abuja.
Buhari ya nuna bakin cikinsa kan mummunan turmutsitsin da ya faru a jihohin da Abuja inda aka rasa rayuka.
Buhari ya jajanta kan iftila'in da ya faru
Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a yau Lahadi 22 ga watan Disambar 2024 a shafin X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar, Buhari ya jajanta wa Gwamna Seyi Makinde da Gwamna Chukwuma Soludo da Minista Nyesom Wike kan lamarin.
Buhari ya bukaci shugabannin su isar da sakon ta'aziyyarsa ga iyalai da abokan wadanda abin ya shafa tare da addu'ar samun sauki ga masu rauni.
Tsohon shugaban ya yi kira ga 'yan Najeriya su yi amfani da lokacin Kirsimeti don tunawa da koyarwar addinin Kirista da ke nuna alheri da yafiya.
Buhari ya taya al'umma murnar bikin Kirsimeti
Buhari ya taya al'ummar Najeriya murnar Kirsimeti tare da fatan sabuwar shekara mai albarka da cigaba ga kowa da kowa.
Buhari ya yi addu'ar Allah ya kawo zaman lafiya, arziki, da lafiya a dukkan sassan kasar nan yayin da ake fatan shiga shekarar 2025.
A karshe, ya roki 'yan Najeriya su kasance masu kaunar juna da yin aiki tare don ci gaban kasar nan baki daya.
Tinubu ya soke bukukuwan da ya shirya
Kun ji cewa shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna takaici bayan aukuwar iftila'in da ya yi sanadin mutuwar mutane a Abuja da Anambra.
Shugaban ya soke bukukuwan da ya shirya a ranar Asabar a jihar Lagos domin girmama wadanda lamarin ya rutsa da su.
Asali: Legit.ng