Jirgin Ruwa Ya Kife da Fasinjoji a Sokoto, An Samu Asarar Rai
- Wani hatsarin jirgin ruwa ya ritsa da fasinjoji 35 a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a ranar Asabar, 21 ga watan Disamban 2024 ya yi sanadiyyar rasuwar wani mutum guda ɗaya
- Masu yin iyo sun samu nasarar ceto ragowar fasinjojin da hatsarin ya ritsa da su bayan jirgin ruwan ya kife da su a tsakiyar rafi
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - An shiga jimami bayan an samu aukuwar wani hatsarin jirgin ruwa a jihar Sokoto.
Hatsarin jirgin ruwan wanda ya auku a ƙauyen Tangwale da ke gundumar Dundaye a jihar Sokoto, ya yi sanadiyyar rasuwar wani dattijo mai shekara 60 da haihuwa.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hatsarin ya auku ne da tsakar rana a ranar Asabar, 21 ga watan Disamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin
Mai ba Gwamna Ahmed Aliyu shawara kan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Alhaji Nasiru Garba Kalambaina ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Alhaji Nasiru Garba Kalambaina ya bayyana cewa fasinjoji 35 ne ke cikin jirgin ruwan lokacin da ya kife.
"Amma masu yin iyo sun samu nasarar ceto mutane 34 da ransu. Ɗaya daga cikin fasinjojin mai shekara 60 ɗan ƙauyen Tangwale, ya rasa ransa, inda daga baya aka ɗauko gawarsa aka binne shi kamar yadda addinin Musulunci ya tanada."
- Alhaji Nasiru Garba Kalambaina
Alhaji Nasiru Garba Kalambaina wanda ya jagoranci wasu jami’an hukumar da hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA zuwa ƙauyen, ya jajantawa iyalan marigayin a madadin gwamnatin jihar Sokoto.
Jirgin ruwa ya kife da fasinjoji a Benue
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jirgin ruwa ya yi hatsari da wasu fasinjoji a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Hatsarin jirgin wanda ya ritsa da mutanen da ke dawowa daga kasuwa ya yi sanadiyyar rasuwar aƙalla mutane 20.
Jirgin ruwan dai ya kife ne sakamakon yawan da mutane suka yi masa da kuma lodin kayayyaki masu yawa da aka cika shi da shi.
Asali: Legit.ng