Wani Kaya Sai Amale: Shugaban Karamar Hukuma Ya Gabatar da Kasafin N7bn

Wani Kaya Sai Amale: Shugaban Karamar Hukuma Ya Gabatar da Kasafin N7bn

  • Shugaban karamar hukumar Ikeja, Mojeed Balogun, ya gabatar da kasafin kudi na Naira biliyan bakwai don shekarar 2025 ga majalisar dokokin yankin
  • Kasafin kudin mai taken "Kasafin ci gaba mai Inganci" ya kunshi dabarun ci gaba da ayyukan samar da hidimomi masu inganci a yankin
  • Shugaban majalisar yankin, Ayotunde Adenuga, ya tabbatar da duba kudirin kasafin da sauri don tabbatar da walwalar jama'a a matakin ƙasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Lagos - Shugaban karamar hukumar Ikeja a jihar Lagos, Mojeed Balogun ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025.

Hon. Balogun ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 ga majalisar dokokin yankin da kudi sama da Naira biliyan bakwai.

Shugaban karamar hukuma ya gabatar da kasafin kudi N7bn
Shugaban karamar hukuma a jihar Lagos ya gabatar da kasafin N7bn. Hoto: Ikeja Voice.
Asali: Facebook

Shugaban karamar hukuma ya gabatar da kasafin kudi

TVC News ta tabbatar cewa an sanya wa kasafin taken "Kasafin ci gaba mai Inganci," wanda ke nuni da tsare-tsare masu ma'ana.

Kara karanta wannan

Atiku ya gano manyan matsaloli 5 a kasafin 2025, ya ba Tinubu muhimmiyar shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, an tabbatar da kasafin zai kawo sauyi da tabbatar da ci gaba mai ɗorewa da hidimomi masu inganci.

Balogun ya bayyana cewa kasafin ya haɗa da shirin kammala ayyukan ci gaba da ake yi tare da fara sabbin ayyuka idan an amince da kudirin cikin lokaci.

Shugaban karamar hukuma ya tabbatar wa majalisar cewa dukkan matakan da aka ɗauka na ci gaba za su amfani jama'a kuma za su haɓaka jin daɗin rayuwarsu.

Shugaban Majalisar yankin ya yabawa kasafin

Shugaban majalisar dokokin yankin, Ayotunde Adenuga, ya nuna goyon bayansa wajen duba kudirin cikin sauri don inganta rayuwar jama'a a yankin.

Adenuga ya ƙara da cewa tattaunawa mai kyau kan kasafin kudi na da muhimmanci don tabbatar da cimma burin kasafin da kuma biyan bukatun jama'a.

Shugaban ya yi kira ga al'umma su goyi bayan gwamnati don ganin an cimma nasarar kasafin cikin lokaci mai kyau da inganci.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ware N27bn domin rabawa Buhari, Jonathan da mataimakansu a 2025

Ciyaman ya gabatar da kasafin kudin 2025

Kun ji cewa Shugaban karamar hukuma a Enugu ya gabatar da kasafin 2025 na N5.5bn, wanda ya zarce N4.153bn da ya gabatar a 2024.

Kasafin kudin ya maida hankali kan manyan ayyuka kamar tituna, lafiya, aikin gona da ilimi, tare da shirin inganta kudin shiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.