Tsohon Babban Alkalin Kotun Koli Ya Rasu a Kebbi, Tinubu Ya Tura Sakon Ta'azziya

Tsohon Babban Alkalin Kotun Koli Ya Rasu a Kebbi, Tinubu Ya Tura Sakon Ta'azziya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rasuwar Mai Shari’a Uthman Muhammad Argungu a matsayin babban rashi ga kasa da kansa.
  • Mai Shari’a Argungu, wanda ya rasu yana da shekaru 90, an binne shi a Argungu, Jljihar Kebbi, bisa koyarwar Musulunci.
  • Shugaba Tinubu ya tuna da rayuwar mai Shari'a, Argungu, wanda ya yi wa Najeriya hidima mai cike da gaskiya da jajircewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nuna alhini kan rasuwar tsohon Mai Shari’a na Kotun Koli, Uthman Muhammad Argungu.

Mai Shari’a Argungu, wanda ya rasu yana da shekaru 90, fitaccen lauya ne kuma aboki na musamman ga Shugaban kasa.

Tsohon alkalin kotun koli ya riga mu gidan gaskiya
Bola Tinubu ya jajanta kan rasuwar tsohon alkalin kotun koli, Uthman Argungu. Hoto: Bayo Onanuga.
Asali: Facebook

Tinubu ya jajanta da tsohon alkali ya rasu

Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa da Fadar shugaban kasa ta wallafa a shafin X a yau Lahadi 22 ga watan Disambar 2024.

Kara karanta wannan

'Ka na kan turba mai kyau': Basarake a Arewa ya yabawa salon mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni aka binne marigayin a yau Lahadi 22 ga watan Disambar 2024 a Argungu da ke jihar Kebbi.

Shugaba Tinubu ya bayyana marigayin a matsayin mai kwazo, wanda ya sadaukar da rayuwarsa don hidima ga ‘yan Adam da kuma Najeriya baki daya.

Tinubu ya tuna gudunmawar marigayin a matsayin malami tun a tsohuwar jihar Sokoto, kafin ya fara shari’a a shekarar 1965.

Daga nan, ya ci gaba da samun daukaka, inda aka nada shi a matsayin Mai Shari’a na Kotun Koli a shekarar 1993.

Tinubu ya yi addu'a ga marigayin

Ba Najeriya kadai ya yi wa aiki ba, domin ya kuma yi aiki a matsayin Mai Shari’a mai ziyara a Kotun Koli ta kasar Gambiya.

Shugaba Tinubu ya yi addu’a Allah ya jikansa, ya kuma ba iyalansa da mutanen Kebbi hakurin jure rashinsa.

Tsohon gwamna, Abbe ya rasu

Kara karanta wannan

Yan majalisa sun saka ranar raba albashinsu ga talakawan Najeriya

Kun ji cewa an tafka babban rashi bayan mutuwar tsohon gwamnan jihar Akwa Ibom, Manjo-janar Godwin Osagie Abbe.

Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 21 ga watan Disambar 2024 a Abuja bayan fama da doguwar jinya.

Kafin rasuwarsa, matsayin ya mulki jihohin Akwa Ibom da Rivers a matsayin soja kafin rike muƙamin Minista.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.