Tinubu, Gwamnoni Sun Halarci Daurin Auren Dan Gwamna, An Kwarara Masa Yabo
- Shugaba Bola Tinubu ya yabawa Gwamna a Najeriya kan jagoranci na kwarai da hada kan al'umma
- Tinubu ya kora yabon ne ga Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta wanda ya kasance dan jam'iyyar PDP
- Shugaban ya fadi haka yayin halartar bikin daurin auren dan Gwamna Oborevwori da aka yi a jihar Delta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Delta - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya halarci daurin auren dan Gwamna Sheriff Oborevwori a Delta.
Tinubu ya bayyana gwamnan a matsayin mai hade kan al’umma da jagoranci na kwarai duba da jama’a daga bangarori daban-daban na siyasa da suka halarci bikin auren dansa a Asaba.
Tinubu ya yabawa salon mulkin Gwamna Oborevwori
Jaridar Thisday ta tabbatar da cewa an daura auren Clinton Oborevwori da masoyiyarsa, Knowledge Davidson.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu, wanda Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya wakilta ya yabawa Gwamna Oborevwori kan kasancewarsa gwamna na kowa da kowa.
Ya ce gwamnan ya kasance mai son zaman lafiya da ba ya nuna bambanci, ya ce idan shugabanni za su guji son zuciya da banbancin siyasa da addini, Najeriya za ta zama kasa mafi kyau ga kowa.
Gwamna Oborevwori, ya nuna godiyarsa ga Tinubu da takwarorinsa gwamnoni da duk wadanda suka halarci bikin don girmama shi da iyalinsa.
Ya bayyana Shugaba Tinubu a matsayin mutum nagari da ba ya kallon bambancin siyasa a mu’amalarsa, cewar Tribune.
Gwamnonin da suka halarci daurin auren
Wadanda suka halarci bikin akwai Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq da gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa.
Sai gwamna Agbu Kefas na Taraba da Douye Diri na Bayelsa da gwamnan Rivers, Sim Fubara da Dapo Abiodun daga Ogun da Caleb Muftwang na jihar Filato da Abiodun Oyebanji na Ekiti da Usman Ododo na Kogi da Hope Uzodimma daga Imo.
Tinubu ya ba da auren yar Barau
Kun ji cewa manyan 'yan siyasa da dattawa sun halarci bikin daurin auren yar Sanata Barau Jibrin a birnin Abuja.
An daura auren ne tsakanin iyalan Sanata Barau da na tsohon Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero a masallacin Abuja.
Asali: Legit.ng