Hankula Sun Tashi da Wata Tankar Mai Ta Tarwatse Ana cikin Jimamin Rasa Rayuka a Abuja
- Mutane da dama sun shiga tashin hankali bayan wani iftila'i da ya faru a jihar Ondo da yammacin yau Asabar
- Hakan ya faru ne bayan wata tankar mai ta kife a bakin titi da ya yi sanadin tashin gobara mai ƙarfi
- Lamarin ya faru ne da misalin karfe 6:30 na yammacin yau a karamar hukumar Odigbo da ke jihar
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ondo - Hankulan al'umma sun tashi bayan wata tanka dauke da mai ta kama da wuta a jihar Ondo.
Lamarin ya faru ne da yammacin yau Asabar 21 ga watan Disambar 2024 a karamar hukumar Odigbo da ke jihar.
Tankar mai ta kone kurmus a Ondo
Kwamandan sashin hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) a jihar, Mista Samuel Ibitoye ya tabbatar da faruwar lamarin ga Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibitoye ya bayyana haka ne a cikin wata tattaunawa ta waya inda ya ce lamarin ya firgita al'ummar yankin matuka.
Ya ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar da ta tashi daga tankar har zuwa wannan lokaci.
Musabbabin abin da ya faru da tankar
Rahotanni sun tabbatar da cewa tankar ta kauce hanya ne inda ta fadi gefen kwalta a bakin wani rami.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa tankar ta kauce daga kan titin, ta fadi a wani rami kusa da hanya.
Bayan tankar ta fadi, wuta ta kama da hayaki mai karfi inda ya mamaye yankin, lamarin da ya haifar da gagarumar matsala ta gani da kuma cunkoson ababen hawa.
Yan sanda 3 sun mutu a mummunan hatsari
A labari mai kama da wannan, kan sanda uku da wata da ake zargi da aikata laifi sun mutu a wani hatsari da ya rutsa da su a Ore da ke ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Wata motar tirela ce ta markaɗe ƴan sandan a lokacin da take gangarowa daga gadar Ore, ɗan sanda ɗaya ya samu munanan raunuka.
Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan Ondo ta ce yanzu haka sun fara gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.
Asali: Legit.ng