Kakakin Majalisa Ya Fadi Abin da Ya Faru kan Kwace Filinsa, Ya Gargadi Hukumar FCTA

Kakakin Majalisa Ya Fadi Abin da Ya Faru kan Kwace Filinsa, Ya Gargadi Hukumar FCTA

  • Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Tajudden Abbas ya yi magana kan rahotanni da ke yawo game da kwace masa fili
  • Hon. Abbas ya ƙaryata labarin da ake yaɗawa inda ya ce kwata-kwata bai cikin wadanda ake bi bashi game da rigimar fili
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa ya fitar inda ya gargadi gidajen jaridu kan yada labarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas ya mayar da martani bayan rahoton kwace masa fili.

Hon. Abbas ya musanta cewa ana binsa bashin kan fili da aka ba shi a Babban Birnin Tarayya kamar yadda ake yadawa.

Kakakin Majalisa ya yi martani kan labarin kwace masa fili a Abuja
Kakakin Majalisa ya musanta labarin kwace masa fili a Abuja inda ya ce ko sisi ba a binsa. Hoto: Hon. Tajudden Abbas.
Asali: Facebook

Tajudden Abbas ya magantu kan kwace masa fili

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Musa Krishi ya fitar, cewar Channels TV.

Kara karanta wannan

Bayan tsokacin shugaban BUA, Dangote ya fadi matsayarsa kan matakan Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Krishi ya bayyana cewa Abbas yana da fili guda daya tilo a Abuja, kuma ya riga ya biya dukkan kudaden da ake binsa.

Ya ce kuskure ne da FCTA ta hada sunan Abbas cikin wadanda ba su biya bashin kudaden filaye ba, lamarin da ya kai ga soke mallakar filayensu.

Hadimin shugaban Majalisar ya shawarci hukumar FCTA da ta dinga taka tsan-tsan wajen tafiyar da irin wadannan al'amura.

Kakakin Majalisa ya ƙaryata labarin kwace masa fili

"Kakakin Majalisar Wakilai Rt. Hon. Abbas Tajudeen ya samu labari game da rahotannin da suka mamaye kafafen watsa labarai, inda aka ce Hukumar FCTA ta soke mallakar filaye na wasu mutane, ciki har da shi saboda rashin biyan kudade."
“Domin fayyace al’amari, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, yana da fili daya kacal da aka ba shi a Abuja, kuma ya riga ya biya kudaden da ake binsa tun watan Oktoba 2024."

Kara karanta wannan

Bayan kwace filayen Buhari da wasu yan siyasa, Wike ya sake ba da wa'adin makwanni 2

“Saboda haka, kuskure ne FCTA ta hada sunansa cikin wadanda ake zargin ba su biya bashin kudaden filaye ba, wanda ya kai ga soke mallakarsu."

- Musa Krishi

Sanarwar ta ce Hon. Abbas ya gargadi kafafen yada labarai da su rika tantance gaskiya kafin yada rahotanni.

Wike ya ba waɗanda aka kwacewa filaye wa'adi

Kun ji cewa bayan soke filayen manyan yan siyasa a Najeriya, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sake ba da wa'adi kan matakin.

Nyesom Wike ya ba da tsawon makwanni biyu ga dukan wadanda ba su cika ka'ida ba su tabbatar sun bi doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.