Bayan Tsokacin Shugaban BUA, Dangote Ya Fadi Matsayarsa kan Matakan Tinubu
- Shahararren dan kasuwa a Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya yabawa salon mulki da tsare-tsaren Bola Tinubu
- Dangote musamman ya yabawa Tinubu kan matakin siyar da danyen mai a kan kudin Naira madadin dala
- Hakan na zuwa ne kwana ɗaya bayan takwaransa, Abdulsamad Rabiu ya yabi shugaban kan matakan da yake dauka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Fitaccen dan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan tsare-tsarensa.
Dangote ya yabi Tinubu kan saukin tattalin arziki da aka samu a tsarin musayar danyen mai da naira ya kawo.
Dangote ya kora yabo ga tsare-tsaren Tinubu
Attajirin ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar 21 ga watan Disambar 2024, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dangote ya ce wannan dabarar ta rage matsin lamba a kasuwar musayar kudade tare da kara samun wadataccen mai inganci da rahusa.
Ya ce sabon tsarin ya ba matatun mai na gida damar siyan danyen mai da naira sannan su sayar da kayayyakin da aka tace a cikin gida.
Ya kara da cewa matatar mai da ta rage farashin mai daga N970 zuwa N899.50 ga dillalai ta kulla yarjejeniya da MRS domin sayar da man fetur a farashin N935 kowace lita.
Dangote ya godewa yan Najeriya kan goyon baya
Fitaccen dan kasuwar ya godewa ‘yan Najeriya bisa goyon bayan da suke ba shi tare da yabawa gwamnati, Daily Post ta ruwaito.
Dan kasuwar ya yabi gwamnatin kan kokarinta na samar da yanayi mai kyau ga bunkasar masana’antar tace mai a cikin gida.
“Don tabbatar da cewa wannan saukin farashin ya kai ga masu amfani, mun kulla yarjejeniya da MRS don sayar da man fetur daga shagunan sayar da man su a duk fadin kasar nan a farashin N935 kowace lita."
"Wannan farashin ya riga ya fara aiki a Lagos, sannan za a fara amfani da shi a duk fadin kasar daga ranar Litinin."
- Aliko Dangote
Shugaban BUA ya yabawa tsare-tsaren Tinubu
Kun ji cewa fitaccen dan kasuwa a Najeriya kuma shugaban kamfanin BUA, Abdulsamad Rabiu ya yabawa salon mulkin Bola Tinubu.
Abdulsamad ya ce tabbas matakan da shugaban ke dauka suna da tsauri amma hakan shi ne kaɗai mafita.
Asali: Legit.ng