Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur, Ya Sauƙaƙawa 'Yan Kasuwa daga N1,020

Kamfanin NNPCL Ya Rage Farashin Man Fetur, Ya Sauƙaƙawa 'Yan Kasuwa daga N1,020

  • NNPCL ya rage farashin fetur daga N1,020 zuwa N899 a kan kowace lita domin tallafawa 'yan kasuwa da rage farashin man a kasa
  • Masu siye daga Warri da Fatakwal za su biya N970, yayin da matatar Dangote da NNPCL suka daidaita farashin litarsu a kan N899
  • 'Yan Najeriya sun yi murna da rage kudin, inda Kabir Rigachikun ya shaidawa Legit Hausa cewa farashin kayan masarufi zai sauko

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin mai na kasa (NNPCL) ya rage farashin fetur daga N1,020 zuwa N899 a kan kowace lita ga masu dauko man daga rumbun ajiya.

Wannan matakin ya biyo bayan rage farashi da matatar man Dangote ta yi kwanakin baya zuwa N899 a kan kowace lita.

'Yan kasuwa sun yi magana yayin da NNPCL ya rage farashin fetur
NNPCL ya rage farashin fetur daga N1,020 zuwa N899 kan kowace lita. Hoto: @nnpclimited
Asali: Facebook

NNPCL ya rage farashin fetur zuwa N899

Ƙungiyar masu sayar da man fetur (PETROAN) ta tabbatar da wannan canjin a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

IPMAN da matatar Dangote sun shiga yarjejeniyar rage farashin fetur zuwa N935

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce, bisa tsarin farashi na yankuna, NNPCL ya tabbatar da cewa 'yan kasuwa za su sayi litar fetur a kan N899 daga yanzu.

Duk da haka, masu siye daga rumbun ajiyar mai na Warri, Oghara, Fatakwal, da Kalaba za su biya N970 kan kowace lita.

Ana sa ran farashin zai ragu a Janairu

Sanarwar ta ce,

"Kamfanin ya rage farashin fetur daga N1,020 zuwa N899, matakin da ake ganin zai taimaka wajen rage farashin kayan masarufi."

Dr Joseph Obele, kakakin PETROAN ya nuna cewa farashin zai ƙara raguwa kafin ƙarshen Janairu 2025, la'akari da faɗuwar farashin ɗanyen mai da ƙarfin da Naira ke yi.

Sai dai har yanzu mai magana da yawun kamfanin na NNPC, Femi Soneye, bai tabbatar da faruwar hakan ba.

Da yake tsokaci, shugaban PETROAN na kasa Billy Harry, ya ce rage farashin zai kawo sauki ga masu ababen hawa da ‘yan Najeriya a lokacin hutun karshen shekara.

Kara karanta wannan

Matatar Ɗangote za ta fara sayar da fetur ga yan Najeriya, ta faɗi sabon farashin lita

'Yan Najeriya sun yi farin ciki

A zantawarmu da Kabir Yusuf Rigachikun, ya shaida mana cewa rage kudin fetur babban ci gaba ne wanda zai iya kawo saukin kayan masarufi.

"Ina da yakinin cewa za a mu saukin kayan masarufi kwanan nan. Dama a kan samu karin kudin kaya idan aka samu karin kudin fetur saboda dakon kayan.
"Yanzu da aka rage farashin man, muna fatan ganin saukin kaya nan ba da jimawa ba, duk da ka san kasar idan kaya suka tashi suna wahalar sauka."

- A cewar Kabir Rigachikun.

Shi ma Aliyu Adamu Safana, ya nuna jin dadinsa kan saukar farashin kayayyakin inda ya ce yanzu al'umma za su samu saukin sufuri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

iiq_pixel