Lokaci Ya Yi: Ɗaliban Jami'ar OOU 3 Sun Gamu da Ajalinsu a Babban Titi a Najeriya
- Hatsarin mota ya laƙume rayukan ɗaliban jami'ar Olabisi Onabanjo University (OOU) da ke Ago Iwoye a jihar Ogun
- Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, SP Omolola Odutola ya ce ɗalibai uku sun mutu, wasu biyu na kwance ana masu magani
- Mummunan hatsarin ya afku n3 sakamakon gudun da ya wuce ƙima da misalin karfe 3:30 na rana a titin Ago-Iwoye zuwa Ilisan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Wani hatsarin mota da ya afku a titin Ago-Iwoye-Ilisan ya zama ajalin dalibai uku na jami'ar Olabisi Onabanjo (OOU) da ke Ago-Iwoye a jihar Ogun.
Mummunan lamarin, wanda ya faru da misalin karfe 3:30 na tsakar rana jiya Juma'a, an danganta shi da gudun wuce gona da iri.
Bayan ɗalibai uku da suka mutu a hatsarin, wasu mutum biyu sun samu raunuka, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ɗaliban OOU 3 sun kwanta dama
Rahotanni sun ce daya daga cikin daliban ya mutu a wurin, yayin da sauran biyun kuma suka rasu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Ago-Iwoye.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ya tabbatar da faruwar hatsarin a wata sanarwa ranar Asabar, 21 ga watan Disamba.
SP Odutola ya bayyana cewa hatsarin ya rutsa ɓe da wata motar ƙirar Opel Safira tare da lambar rijista ta jihar Lagos AAA-126HE.
Ƴan sanda sun bayyana abin da ya faru
"Wani hatsarin mota ya faru ranar 20 ga Disamba, 2024, da misalin karfe 3:30 na rana a kan titin Ilisan/Ago Iwoye.
"Wani fasinja namiji wanda har yanzu ba a tabbatar da ko wanene ba amma ana kyautata zaton dalibin jami'ar OOU ne ya mutu a wurin. An kai gawarsa babban asibitin Ijebu Ode dakin ajiyar gawa."
"Haka nan wasu ɗaliban jami'ar mata guda biyu sun ce ga garinku nan bayan an garzaya da su asibiti domin kula da lafiyarsu."
- SP Omolola Odutola.
Kakakin ƴan sandan ya ce wasu daliban OOU guda biyu na kwance ana kulawa da lafiyarsu a asibitin jami'ar.
A wani labarin, kun ji cewa wani mummunan hatsari ya rutsa da motar da ke jigilar ɗaliban jami'ar jihar Borno a Arewa maso Gabas.
An ruwaito cewa nutum 3 da ake zaton ɗalibai ne sun rasa rayukansu a hatsarin yayin da wasu mutum 30 ke kwance a asibiti ana masu magani.
Asali: Legit.ng