NNPCL Ya Rufe Matatar Fatakawal da Gwamnati Ta Gyara Kwanan Nan? Gaskiya Ta Fito

NNPCL Ya Rufe Matatar Fatakawal da Gwamnati Ta Gyara Kwanan Nan? Gaskiya Ta Fito

  • Kamfanin NNPC ya yi martani kan rahoton da ake yadawa a soshiyal midiya cewa an rufe matatar man Fatakwal da aka gyara
  • A sanarwar da NNPCL ya fitar a ranar Asabar, 21 ga watan Disamba, kamfanin ya ce masu adawa da matatar ke yada jita jitar
  • Tsofaffin shugabannin NNPC sun tabbatar da cewa matatar Fatakwal tana aiki, yayin da aka tabbatar da shirin dagon kayan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL) ya karyata rahotannin da ke cewa an rufe matatar man Fatakwal da aka gyara kwanan nan

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na NNPC, Olufemi Soneye, ya fitar ranar Asabar, ya bayyana cewa matatar na aiki yadda ya kamata.

Kamfanin NNPCL ya yi magana kan zargin rufe matatar man Fatakwal.
NNPCL ya karyata rahotannin da ake yadawa na cewa ya rufe matatar Fatakwal. Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

NNPCL ya rufe matatar man fatakwal?

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Sanarwar ta da aka fitar a shafin NNPCL na X ta ce shirye-shiryen lodin mai yau na ci gaba, kuma rahotannin da ke cewa an rufe matatar ba gaskiya ba ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsofaffin shugabannin NNPC sun tabbatar da cewa matatar Fatakwal na aiki, kamar yadda suka ziyarta kwanaki kaɗan da suka wuce.

"Hankalin NNPC Limited ya karkata kan wasu rahotanni da ke cewa an rufe tsohuwar matatar Fatakwal, da aka dawo da aikinta watanni biyu da suka wuce."

- A cewar sanarwar Olufemi Soneye.

NNPCL ta nemi alfarmar 'yan Najeriya

Sanarwar ta ci gaba da cwa:

"Muna so mu tabbatar wa jama’a cewa waɗannan rahotanni ba gaskiya ba ne, matatar na aiki yadda ya kamata, kuma shirye-shiryen lodin kaya na ci gaba.
"Muna kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan rahotanni marasa tushe da suka fito daga waɗanda ke son haifar da ƙarancin man fetur domin cutar da ‘yan Najeriya."

Kara karanta wannan

Sojoji sun cafke hatsabiban shugabannin 'yan bindiga, an saki sunayen miyagun

Karanta sanarwar a kasa:

NNPCL ya gyara matatar man Fatakwal

Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto cewa kamfanin NNPCL ya ta da matatar man Fatakwal tare da fara aiki da ita a ranar 26 ga Nuwamba, 2024, bayan an kashe dala biliyan 1.5.

Matatar a halin yanzu tana samar da nau'ikan albarkatun mai da suka hada da man fetur, dizal, kananzir, da kuma iskar gas.

Shugaba Bola Tinubu, majalisar tarayya, 'yan kasuwar mai da sauran masu ruwa da tsaki da ma 'yan Najeriya sun jinjinawa NNPCL kan gyara matatar Fatakwal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.