"N50,000 Duk Wata": Gwamna Ya Tuna da Matasa, Ya Fara Rabon Miliyoyin Naira

"N50,000 Duk Wata": Gwamna Ya Tuna da Matasa, Ya Fara Rabon Miliyoyin Naira

  • Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya rabawa dubban matasa tallafin Naira miliyan 750 a faɗin kananan hukumomin Akwa Ibom
  • Kowane matashi da ya ci gajiyar wannan tallafi na kasuwanci ya samu N50,000 daga mai girma gwamna domin ya kama sana'a
  • Gwamna Eno ya ce wannan shiri wani ɓangare ne na kokarin da gwamnatinsa take yi da nufin ragewa matasa raɗaɗin halin da suke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno ya raba tallafin kasuwanci ga matasa marasa aikin yi akalla 15,000 a faɗin kananan hukumomi 31 na jihar Akwa Ibom.

Gwamna Eno ya rabawa masu Naira miliyam 750 domin su dogara da kansu da kuma rage radaɗin halin kuncin da ake ciki a ƙasar nan.

Gwamna Umo Eno.
Gwamnan jihar Akwa Ibom ya rabawa matasa tallafin Naira miliyan 750 Hoto: Umo Eno
Asali: Facebook

Leadership ta ruwaito cewa shirin tallafin ya bai wa kowane ɗaya daga cikin matasa 15,000 da aka zaɓa N50,000 duk wata.

Kara karanta wannan

Karyar ƴan bindiga da sauran miyagu ta kare a Najeriya, sanata ya hango shirin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Eno ya rabawa matasa N50,000

Sai dai gwamnan ya ce yana shirin faɗaɗa tallafin daga matasa 5,000 zuwa akalla mutum 60,000 a faɗin jihar Akwa Ibom, rahoton TVC News.

Da yake jawabi a wurin kaddamar da fara rabon tallafin, Gwamna Umo Eno ya ce wannan shirin na ɗaya daga cikin kudirorinsa na tallafawa matasa su dogara da kansu.

Ya bukaci wadanda suka ci gajiyar shirin su yi amfani da tallafin ta hanyar fara sana’o’i masu inganci da za su taimaki kansu da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Gwamna zai ɗauki sababbin ma'aikata

Fasto Eno ya kuma tabbatar da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen buɗe kofofin damarmaki ga matasa domin su nuna basirar da Allah ya ba su.

"Wannan shirin wani ɓangare ne na kokarin da muke don tallafawa matasa masu hazaƙa da jajircewa a jihar Akwa Ibom," in ji shi.

Gwamna Eno ya kuma bayyana shirin daukar sababbin ma'aikata, wanda za a fara nan ba da jimawa ba ta shafin yanzar gizo na samarwa matasa aikin yi na jihar (YEP).

Kara karanta wannan

Gwamna zai raba tallafin Naira biliyan 3.9, za a ba jama'a katin cire kudi

Gwamna Eno ya gindaya sharadi ga ma'aikata

A wani labarin kun ji cewa gwamnan Akwa Ibom ya ce ba zai fara biyan sabon mafi ƙarancin albashin N80,000 ba har sai ya gama tantance ma'aikata.

Fasto Umo Eno ya ce babu wata barazana da za ta sa ya sauya tsarinsa kuma su kansu ƴan kwadago suna cikin kwamitin tantancewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262