Dalilin da Ya Sa Gwamnan Zamfara Ya Kinkimo Aikin Gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa
- Gwamnan Zamfara ya ce ya tattago aikin gina filin jirgin sama na kasa da ƙasa ne domin jawo masu zuba hannun jari a jihar
- Dauda Lawal ya ce babu wani ɗan kasuwa da zai sauka a Kano ko Abuja kuma ya share tafiyar sa'o'i akalla bakwai a titin zuwa Zamfara
- Ya ce matsalar tsaro kaɗai ta zama barazana shiyasa ya ga ya dace a gina filin jirgin sama domin sauƙakaka hanyar zirga-zirga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara - Gwamna Dauda Lawal ya bayyana wasu dalilai da suka ja hankalinsa ya kinkimo aikin gina filin sauka da tashin jiragen sama na ƙasa da ƙasa.
Gwamna Dauda ya ce kokarin jawo hankalin masu zuba hannun jarida na cikin dalilansa na gina filin jirgin ƙasa da ƙasa a Zamfara.
Dauda Lawal ya bayyana haka ne da yake amsa tambayoyin manema labarai a Gusau, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin gina filin jirgin sama a Zamfara
Ya ce babu wani ɗan kasuwa mai zuba hannun jari da zai yarda ya shafe sa'o'i bakwai a kan titi zuwa Zamfara saboda babu filin jirgin sama.
"Mun fahimci duk yadda muke son kawo ci gaba, duk yadda muke son jawo masu zuba jari, babu wani mai hankali da zai sauka a Abuja ko Kano kuma ya kamo hanya a mota zuwa Zamfara."
"Rashin tsaro ne babban abin damuwa, don haka babu wani dan kasuwa da zai dauki kudinsa ya zo ya zuba jari a Zamfara, la’akari da cewa sai ya yi tafiyar sama da sa’o’i bakwai a titi kafin ya iso nan."
"Mun fahimci cewa muna bukatar bude jihar, kuma hanya daya tilo ita ce a saukaka zirga-zirga, inda kowa zai iya tahowa a jirgin sama ya shigo Zamfara."
- Dauda Lawal.
Gwamnan Zamfara zai gina filin jirgi
Gwamnan ya ce da farko gwamnatinsa ta so ya zama filin saukar jiragen saman dakon kaya ne kawai, amma daga baya ta gane cewa akwai bukatar a wuce haka.
A cewarsa, daga bisani ya yanke gina filin jirgin da zai haɗa duka biyu, za a riƙa harkokin sufuri da kuma dakon kaya.
Dauda Lawal ya fara rabon tallafi
A wani rahoton, an ji cewa Gwamna Dauda Lawal ya fara rabon tallafi ga marasa galihu da talakawa a faɗin jihar Zamfara.
Gwamnatin Zamfara ta ware sama da Naira biliyan 4 domin rabawa maɓuƙata allafin ƙarƙashin shirin NG Cares a kananan hukumomi 14.
Asali: Legit.ng