Ana Jimamin Mutuwar Yara 32 a Wurin Nishaɗi, Ibtila'i Ya Sake Afkawa Mutane a Ibadan

Ana Jimamin Mutuwar Yara 32 a Wurin Nishaɗi, Ibtila'i Ya Sake Afkawa Mutane a Ibadan

  • Al'ummar jihar Oyo sun sake wayar gari da wata sabuwar jarabawa bayan abin da ya faru a taron nishaɗi na kananan yara a Ibadan
  • An ruwaito cewa gobara ta kama rigi-rigi a kasuwar sayar da kayan gyara ta Araromi da ke Agodi Gate da sanyin safiyar yau Asabar
  • Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar Oyo ya ce har ƴanzu jami'ansu na ƙoƙarin shawo kan gobarar, ya kuma nemi a kawo masu agaji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Oyo - Gobara mai ƙarfi ta kama a shahararriyar kasuwar sayar da kayan gyara ta Araromi da ke Agodi-Gate a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Rahotanni sun nuna cewa zuwa yanzu mummunar gobarar ta laƙume kadarorin ƴan kasuwa da suka kai darajar miliyoyin Naira.

Taswirar jihar Oyo.
Gobara ta kama rigi-rigi a kasuwar sayar da kayan gyara a Ibadan Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2 na safiyar yau Asabar kuma tana ci gaba da ruruwa da yaɗuwa a kasuwar duk da jami’an kwana-kwana na kokarin shawo kanta.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gobarar ta ci ƙarfin jami'an kwana-kwana

Babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Akinyemi Akinyinka ya tabbatar da faruwar lamarin ga jaridar Punch yau Asabar.

Ya ce har yanzun jami'an hukumar na ci gaba da kokawar shawon kan wutar, inda ya buƙaci motocin ruwa su kawo masu ɗauki.

"Muna ta fama da wata mummunar gobara da ta tashi a Agodi-Gate, a taimaka mana a kira motocin ruwa su kawo mana agaji.
"Har yanzun jami'anmu na nan suna ƙoƙarin kashe wutar da ta kama, gobarar ta yaɗu da yawa," in ji shi.

Menene dalilin fashin mummunar gobara?

Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar ba yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da jihar Oyo ke ci gaba da jimamin rasuwar kananan yara sama da 30 a wani turmutsitsi da ya auku a taron nishaɗi.

Yan sanda sun kama tsohuwar matar sarki

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

A wani rahoton, mun kawo maku cewa dakarun ƴan sanda sun cafke tsohuwar matar Ooni na Ife da wasu mutum bakwai kan turmutsitsin da ya yi ajalin yara a Ibadan.

Rundunar ƴan sanda reshen jihar Oyo ta tabbatar da fara bincike kan lamarin, inda ta bai wa iyayen yaran tabbacin samun adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262