Kotu Ta Yanke Hukunci kan MTN, Ta Ci Tararsa N15m kan Cire Kudi Babu Ka'ida
- Wani dan Najeriya ya shigar da kamfanin sadarwa na MTN kara a gaban kotu kan cire masa kudi babu izininsa
- Mutumin mai suna Ezugwu Anene ya yi korafi game da dabi'ar MTN na cire kudi ba tare da mutum ya yi rijista da wani sabis ba
- Daga bisani Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta umarci kamfanin ya biya diyyar N15m saboda saba ka'ida da kuma zamba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta yi hukunci kan korafin da aka shigar da kamfanin MTN a Najeriya.
Kotun ta umarci kamfanin sadarwa, MTN Nigeria da ya biya diyyar N15m bisa cire kudi daga asusun wani abokin hulɗa ba tare da izininsa ba.

Source: Facebook
Kotu ta ci tarar kamfanin MTN N15m
The Nation ta ce hakan ya biyo bayan shigar da korafi da wani abokin hulda, Ezugwu Anene ya yi inda ya ce an cire masa kudi kan sabis ɗin da bai yi rijista ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan hukuncin ya fito ne daga kwamitin alkalan kotun daukaka kara mai mambobi uku, wanda Mai shari’a Okon Abang ya jagoranta.
Mai Shari'a, Abang ya karanto karar a ranar Juma’a 20 ga watan Disambar 2024 kan korafe-korafen.
Kotun ta bayyana cewa cire kuɗi daga asusun abokan hulɗa domin sabis na sabunta rajista ba tare da izini ba, haramun ne kuma ya zama wani nau’i na zamba.
Kotu ta gargadi MTN kan tura sakwanni
Har ila yau, kotun ta ce aika saƙonnin kar-ta-kwana ba tare da izininsu ba ya saba wa hakkinsu na sirri da kuma ya saba ka'ida bisa tanadin Sashe na 37 na kundin tsarin mulkin Najeriya.
Kotun ta kuma jaddada cewa saƙonnin kar-ta-kwana marasa izini sun haifar da damuwa ga mai shigar da ƙara.
Ta kara da cewa MTN na iya samun gagarumin riba daga wannan dabi’a, amma ‘yan Najeriya ba su sani ba, cewar Tribune.
Tun farko kotun ta jingine tarar N300,000 kan MTN inda mai korafi ya ce an shafe shekaru ana cire masa N20 da zarar sako ya shigo wayarsa da sauran abubuwan da bai sai da su ba.
Sai dai kamfanin MTN ya kalubalanci tarar inda ya ce kwata-kwata abin da ya cire daga layin Anene N14,000 ne.
Legit Hausa ta tattauna da wani matashi
Wani tsohon abokin hulɗar MTN ya bayyana yadda karfi da yaji suka sanya shi mayar da layinsa na Airtel.
Muhammad Adamu Kwairi ya ce ya yi korafi ga kamfanin har ya gaji amma ba su daina cire masa kudi ba.
"A lokacin ban san za a iya shigar da su kotu ba kuma na yi tunanin zan sha wahala kafin kwatar ya hakkina."
"Daga ƙarshe, wani ya ba ni shawara na yi gaggawar sauya shi zuwa layin Airtel domin samun sauki kan abin da suke yi min."
- Adamu Kwairi
Kamfanin MTN ya yi gagarumar asara
Kun ji cewa Kamfanin sadarwa na MTN ya bayyana cewa ya yi asarar N514.9bn (bayan an cire haraji) a cikin watanni tara na shekarar 2024.
A rahoton kudi na zango na uku da MTN ya fitar, kamfanin ya ce asarar ta ragu da N4.1bn idan aka kwatanta da zango na biyu.
Asali: Legit.ng

