A Ƙarshe, Tsohon Gwamnan Kogi Ya Fito daga Gidan Kaso bayan Gindaya Masa Sharuda

A Ƙarshe, Tsohon Gwamnan Kogi Ya Fito daga Gidan Kaso bayan Gindaya Masa Sharuda

  • A daren yau Juma'a 20 ga watan Disambar 2024 aka saki tsohon gwamnan jihar Kano, Yahaya Bello daga gidan kaso
  • An saki Yahaya Bello ne bayan cika dukan ka'idojin beli da aka gindaya masa kan zarge-zarge game da badakalar kudi
  • Hakan ya biyo bayan ba da belin tsohon gwamnan da kotu ta yi kan N500m a ranar Alhamis 19 ga watan Disambar 2024

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya shaki iskar yanci bayan cika ka'idojin beli da aka gindaya masa.

An saki tsohon gwamnan ne daga gidan yarin Kuje bayan cika sharuddan beli da Kotun Babban birnin Tarayya da ke Maitama a Abuja da gindaya.

An saki Yahaya Bello daga gidan yari a Abuja
Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya shaki iskar yanci bayan cika sharuda. Hoto: Yahaya Bello.
Asali: Facebook

An ba da belin tsohon gwamna, Yahaya Bello

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya ce bayan Wike ya kwace filinsa da na wasu manya a Abuja

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar gyaran hali, Adamu Duza ya fitar, cewar Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan ba da belinsa da Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi a yayin zamanta na ranar Alhamis, 19 ga watan Disambar 2024.

Kotun ta ba da belin Yahaya Bello a kan kuɗi N500m tare da kawo mutum uku waɗanda za su tsaya masa.

Yahaya Bello ya fito daga gidan yari

Adamu Duza ya ce an saki Yahaya Bello ne duba da cika sharudan beli da aka gindaya masa, Tribune ta ruwaito.

"An saki Yahaya Bello bayan ya cika sharuddan beli, an sake shi a daren yau Juma’a 20 ga watan Disambar 2024."
“Shugaban hukumar gyaran hali a Abuja, Ajibogun Olatubosun ya kasance a wurin domin tabbatar da cewa an sake shi cikin kwanciyar hankali tare da bin dukkan dokoki.”

- Adamu Duza

Kara karanta wannan

Badakalar N110.4bn: Kotu ta ba da belin Yahaya Bello, ta gindaya sharudda

Yahaya Bello ya musanta zarginsa da ake yi

A baya, kun ji cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello ya musanta tuhumar da ake yi masa ta karkatar da Naira biliyan 80 daga asusun gwamnatin Kogi.

Hukumar EFCC ta gurfanar da Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan tuhume-tuhume 19 na zamba.

Sai dai a zaman kotun a ranar Juma'a, 13 ga watan Disamba, Mai shari'a Emeka Nwite ya karɓi uzurin lauyan EFCC na janye wata buƙata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.