Bayan Umarnin Tinubu, Jiragen Ƙasa Sun Fara Ɗaukar Fasinjoji Kyauta a Najeriya
- Gwamnatin tarayya fara ɗaukar fasinjojin jirgin ƙasa kyauta domin sauƙaƙa wa ƴan Najeriya a bukukuwan Kirismeti da sabuwar shekara
- Hakan dai ya biyo bayan umarnin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar na jigilar mutane kyauta daga nan zuwa watan Janairu
- Mukaddashin shugaban hukumar NRC ya ce sun fara ɗaukar matakan tabbatar da tsaron rayukan fasinjojin jiragen ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kamar yadda shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni, jiragen ƙasa sun fara jigilar ƴan Najeriya kyauta saboda zuwan kirismeti.
Gwamnatin tarayya ta fara ɗaukar fasinjojin jiragen kasa zuwa wurare daban-daban kyauta a faɗin Najeriya domin saukakawa ƴan Najeriya.
Muƙaddashin manajan darakta na hukumar sufurin jiragen kasa (NRC), Ben Iloanusi shi ne ya tabbatar da fara jigilar kyauta, Daily Trust ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kirismeti: Jiragen kasa sun fara aiki kyauta
Yayin da ya tarbi rukunin farko na fasinjojin a tashar jirgin kasa ta Kubwa, Abuja daga Rigasa, ya ce mutane sun nuna damuwa kan yanayin tsaro.
Ya ce hukumar NRC ta fara ɗaukar matakan da suka dace domin magance damuwar tsaro da fasinjoji suka koka a kai tun a ranar farko.
A rahoton The Nation, Ben Iloanusi ya ce:
"Kowace rana za a samu fasinjoji 20,000 kuma gwamnatin tarayya ta yi ƙiyasin jigilar ƴan Najeriya 340,000 kyauta daga nan zuwa lokacin da garaɓasar za ta ƙare a farkon watan Janairu."
NRC ta jero tashoshin jirgin ƙasa 5
Ya ƙara da cewa za a gudanar da wannan aikin sufuri kyauta ne a layukan dogo biyar da suka haɗa da Kaduna-Abuja, Lagos-Ibadan, Warri-Itakpe, Fatakwal-Aba da na Legas.
Da aka tambaye shi ko me hukumar NRC ke yi domin daƙile ƴan haɗama, masu sayen tikiti fiye da ɗaya, shugaban NRC ya ce:
"Shafinmu na nan a yanar gizo kuma yana aiki yadda ya kamata, mun ɗauki matakai kuma mina iya bakin kokarinmu wajen magance sayen tikiti fiye da ɗaya."
Tinubu da Shettima za su kashe N9bn
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima za su kashe sama da Naira biliyan 9 a tafiye-tafiye kurum a shekarar 2025.
Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan da ke kunshe a kasafin kudin 2025 da Bola Tinubu ya gaɓatar a a Majalisar tarayya ranar Laraba.
Asali: Legit.ng