Kirsimeti: Gwamna a Arewa Ya Ware Tirelolin Shinkafa 100 domin Rabawa Al'umma
- Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya tausayawa al'ummar jiharsa yayin da ake shirin bikin Kirsimeti
- Gwamnan ya ware manyan motoci na shinkafa har guda 100 domin rabawa ga al'ummar jihar
- Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Kiristoci ke shirin bikin Kirsimeti a ranar 25 ga watan Disambar 2024
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo ya tallafawa al'umma ana shirin bikin Kirsimeti.
Gwamnan ya raba sama da tirela 100 cike da shinkafa domin murnar bikin Kirsimeti da sabuwar shekara ga iyalai.
Gwamna Ododo ya raba shinkafar Kirismeti
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kwamishinan yafa labarai, Kingsley Fanwo ya fitar, cewar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce wannan kyauta an yi ta ne domin rage nauyin tsadar kayayyaki a lokacin bukukuwan.
Fanwo ya ce wannan shiri ya tabbatar da jajircewar Gwamna Ododo wajen kula da walwalar jama’a.
“Ina tabbatar muku cewa gwamnan talakawa, Ahmed Usman Ododo ya karbi sama da motoci 100 dauke da shinkafa."
"An ware shinkafar domin bukukuwan Kirsimeti a dukkan kananan hukumomi 21 na jihar."
"Wannan ya tabbatar da cewa iyalai a jihar za su samu damar jin dadin bukukuwan Kirsimeti da karshen shekara."
- Kingsley Fanwo
Gwamna ya ba da umarnin biyan albashi
Fanwo ya kara da cewa, gwamnan, baya ga wannan tallafi, ya tabbatar da biyan albashi ga ma’aikatan gwamnati a ranar 14 ga Disambar 2024.
Har ila yau, gwamnan ya samar da tallafi ga mazauna jihar da ba ma’aikatan gwamnati ba, Daily Post ta ruwaito.
Rahotanni sun nuna cewa rabon shinkafar ya haifar da farin ciki a tsakanin al'umma, inda da dama suka yaba da shugabancin da jin kai na gwamnan.
Gwamna Ododo ya rufe kasuwa a Kogi
Kun ji cewa Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo ya ba da umarnin rufe kasuwar Zango saboda taɓarɓarewar tsaro a yankin Osara.
Kwamishinan yaɗa labarai, Kingsley Fanwo ya ce gwamna ya ɗauki wannan matakin ne bayan gano ana ɓoye ƴan ta'adda a kasuwar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng