Lokaci Ya Yi: Ƴan Sanda 3 Sun Gamu da Ajalinsu yayin da Suka Je Kama Wata Mata
- Yan sanda uku da wata da ake zargi da aikata laifi sun mutu a wani hatsari da ya rutsa da su a Ore da ke ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo
- Wata motar tirela ce ta markaɗe ƴan sandan a lokacin da take gangarowa daga gadar Ore, ɗan sanda ɗaya ya samu munanan raunuka
- Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar ƴan sandan Ondo ta ce yanzu haka sun fara gudanar da bincike don gano abin da ya haddasa hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Wata babbar motar tirela ta murkushe akalla mutum huɗu har lahira a Ore da ke ƙaramar hukumar Odigbo ta jihar Ondo.
Rahotanni sun nuna cewa mutum uku daga cikin waɗanda suka mutu a hatsarin jami'an rundunar ƴan sanda ne a jihar.
Jaridar Leadership ta tattaro cewa jami’an da suka rasa rayukansu a hatssrin suna aiki ne a sashin sa ido na rundunar ƴan sandan Ondo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun mutu a hatsari
An ce sun baro hedkwatar ƴan sanda da ke Akure ne domin cafke wata mai laifi a yankin Ore, bisa rashin sa'a suka gamu da ajalinsu.
Wani ganau ya bayyana cewa tirelar ta kufce wa direba ne yayin da take gangarowa daga gadar Ore, inda ta markaɗe motar ƴan sanda da ke gefe.
Nan take ƴan sanda uku da wata mace da suka kamo suka mutu yayin da ragowar ɗan sanda ɗaya ke kwance a asibiti ana masa maganin raunuka.
Wane mataki rundunar ƴan sanda ta ɗauka?
Da aka tuntubi jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar Ondo (PPRO), Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta tabbatar da faruwar lamarin.
Odunlami-Omisanya ta ƙara da cewa rundunar ‘yan sandan ta fara gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa aukuwar hatsarin har aka rasa rayuka.
Motar jami'ar jihar Borno ta yi hatsari
Kun ji cewa wata motar bas da ke aiki a jami'ar jihar Borno ta gamu da hatsari, mutum 3 sun riga mu gidan gaskiya.
An ruwaito cewa bayan rasa rayuka a mummunan hatsarin, wasu mutane 30 sun samu raunuka kala daban-daban.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng