Tsohon Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzaga, Ya Tona Yadda Aka Rugurguza Arewa

Tsohon Shugaban Majalisa Ya Yi Zazzaga, Ya Tona Yadda Aka Rugurguza Arewa

  • Tsohon shugaban majalsar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bayyana goyon bayansa ga kudirin harajin Bola Ahmed Tinubu
  • Haka kuma tsohon dan majalisar ya dora laifin lalacewar tattalin arzikin Najeriya a kan gazawar shugabannin Arewacin Najeriya
  • Ya shawarci 'yan Najeriya da su guje wa yawan sukar gwamnatin APC da Tinubu ke jagoranta tare da mara wa shirye-shiryenta baya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Tsohon Shugaban majalisar Dokokin tarayya,Yakubu Dogara, ya bayyana dalilin da ake samun rashin ci gaba a Arewa.

Rt. Hon Yakubu Dogara ya danganta halin da Arewa ke ciki na rashin ci gaba da shugabannin yankin.

Dogara
Tsohon shugaban majalisa ya zargi shugabannin Arewa da jawo wa shiyyar matsala Hoto: Hon. Yakubu Dogara
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Dogara ya yi wannan batu ne a tattaunawa na shugabannin Kiristoci a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya tashi da jin labarin mutuwar yara 35, ya ba gwamna sabon umarni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Yadda shugabanni su ka lalata Arewa,” Dogara

Trust radio ta wallafa cewa Bukola Saraki ya bayyana cewa shugabanni daga Arewa sun rasa damar ciyar da yankin gaba.

Ya shawarci ‘yan kasar nan da su bar sukar gwamnatin Bola Tinubu ganin yadda aka jagororinsu su ka lalata shiyyar a shekara 40.

"Ya kamata a bayyana cewa Shugaba Tinubu ko Kudu ba shi ne matsalar mu ba.
Wasu na ikirarin cewa Yarbawa suna samun nadin mukamai, amma mu yi tunani. Mun yi mulki a wannan ƙasa fiye da shekaru 40 lokacin da 'yan Arewa ke kan mulki. Me muka cimma? Arewa tana nan daidai, tana cikin talauci saboda shugabanninmu na cikin gida."

Yakubu Dogara ya nemi a gyara Najeriya

Tsohon shugaban majalisa, Bukola Saraki ya bukaci 'yan Najeriya da su tallafa wa Shugaba Bola Tinubu wajen canza kasar nan.

Ya ce za a iya haka ne ta hanyar goyon bayan dokokin gyaran haraji da ke jiran amincewar majalisar dokoki.

Kara karanta wannan

Gwamna da wasu ƙusoshi sun sake taso da Batun Tsige Shugaban PDP na ƙasa

Tinubu: Yakubu Dogara ya yabi Gwamnati

A wani labarin, kun ji tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya bayyana cewa ya na goyon bayan matakan da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke bijirowa da su wajen samar da ci gaba.

Tsohon dan majalisar ya bayyana cewa Tinubu ya nuna jarumta a wajen magance matsalolin Najeriya duk kuwa da kalubalen da hakan ya ke jawo wa, kamar matsalar kudi da 'yan kasa ke gani.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng