Karancin Takardan Kudi: Kungiyar NLC Ta Dira a kan Gwamnatin Bola Tinubu

Karancin Takardan Kudi: Kungiyar NLC Ta Dira a kan Gwamnatin Bola Tinubu

  • Yayin da ake shirin fara bukukuwan karshen shekara, Kirsimeti da ta sabuwar shekara, takardun kudi na kara ja baya
  • Wasu daga cikin mazauna Kano sun shaida wa Legit cewa su na tuntubar wurin da su ke yawan cirar kudi don a ajiye masu
  • Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta nemi shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta tsoma baki a cikin matsalar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Imo - Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki kan matsalar karancin kudi a Najeriya.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bayyana hakan a wata takardar bayan taro da ya rattaba hannu tare da Emmanuel Ugboaja, babban sakataren kungiyar.

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Tinubu
NLC ta nemi a kawo karshen karancin kudi Hoto: Bayo Onanuga/Nigeria Labor Congress
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa an fitar da takardar bayan taron ne bayan kammala taron Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) da aka gudanar a Owerri.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a sun koka da karancin kudi

Wasu daga cikin mazauna Kano sun shaida wa Legit cewa sun fi amfani da katinsu wajen sayen abubuwan da su ke bukata saboda karancin takardun kudi.

Salma Muhd ta shaida cewa;

Ko abin wanki zan saya ko gishiri, sai na ba yara na katin ATM na opay su je su sayo, sannan a kara masu da N500 ko N1000.
Yanzu idan na je POS ma sai su ce babu kudi, sai dai na je na dawo, shi ya sa kudin mota kawai na ke karba yanzu.

Ana neman takardun kudi an rasa

Tukur Hamisu, wani mai sayar da kayan lemo da sana'ar POS ne a Kano, ya bayyana cewa abokan huldarsa kan kira shi don ya ajiye masu takardun kudi.

Kara karanta wannan

Fafaroma ya fadi yadda ya tsallake harin kunar bakin wake sau 2 a kasar Iraqi

Sanarwar NLC ta bayyana rashin jin dadin rashin kudin, inda ta kara da cewa;

“NLC na neman gwamnatin tarayya ta gaggauta daukar mataki don gyara wannan matsala ta tsarin aiki da kare hakkin kudi na ‘yan kasa.

CBN ya zargi bankuna da jawo rashin kudi

A baya kun ji cewa Babban bankin kasar nan (CBN) ya kaddamar da bincike a kan matsalolin da ke jawo karancin kudi a tsakanin 'yan Najeriya, lamarin da ke kara kamari sosai.

CBN ya dora alhakin raguwar takardun kudi a kan bankunan 'yan kasuwar da su ka fifita wasu daga cikin abokan huldarsu a kan bai wa sauran jama'ar gari kudin da su ke da bukata.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

iiq_pixel