Sojoji Sun Cafke Hatsabiban Shugabannin 'Yan Bindiga, An Saki Sunayen Miyagun
- Dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara wajen kama kasurgurman 'yan bindiga a kasar nan
- Daraktan yaɗa labarai na DHQ, Manjo Janar Buba ne ya tabbatar da kama manyan 'yan ta'adda a Arewacin Najeriya
- Ya ce an kama shugabannin 'yan ta'adda guda biyu da suka hada da Hamisu Sale da Abubakar Muhammad
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Hedikwatar tsaro (DHQ) ta bayyana cewa sojoji sun kama manyan shugabanni 'yan ta'adda guda uku tare da wasu 269 cikin mako guda. A cikin wannan adadi, an kashe 'yan ta'adda 212 a cikin wannan lokaci kawai, a lokacin da dakarun ke yaki da ta'addanci a fadin kasar.
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa mai magana da yawun rundunar tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan.
Sojoji sun ceto wadanda aka sace
Jaridar The Guardian ta bayyana cewa Hedikwatar Tsaro ta bayyana cewa a arewa ta tsakiya da arewa maso yamma, an kubutar da mutane 152 da aka sace. Manjo Janar Buba ya ce an kama shugabannin 'yan ta'adda guda biyu da aka gano, wato Hamisu Sale (Master) da Abubakar Muhammad a Arewa ta Tsakiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga na taimaka wa sojoji
Hedkwatar Tsaro ta bayyana cewa 'yan ta'adda biyu da aka kama suna ba da hadin kai tare da samar da muhimman bayanai game da tsarin ayyukansu. Manjo Janar Buba ya ce an kama wani babban shugaba kuma shahararren dan ta'adda mai suna Bako Wurgi a yankin arewa maso yamma.
Sannan ya kara da cewa a cikin makon nan, dakarun sojojin kashe 'yan ta’adda 212 tare da kama mutane 272.
Sojoji sun samu nasara a kan 'yan ta'adda
A baya mun ruwaito cewa Hedkwatar tsaron kasar nan ta bayyana yadda ta samu nasarar ragargaza 'yan ta'adda da su ka addabi jama'a tare a lokacin da 'yan ta'adda su ka rike wuta.
Daraktan yaɗa labarai na DHQ ya bayyana cewa an hallaka 'yan ta'adda akalla 8,034 yayin da ake ci gaba da ruwan wuta domin magance matsalar tsaro a Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng