Gwamnati Tinubu za Ta Kashe N59.4b don Farfado da Aikin Shekaru 24 a Jigawa

Gwamnati Tinubu za Ta Kashe N59.4b don Farfado da Aikin Shekaru 24 a Jigawa

  • Gwamnatin tarayya ta ware biliyoyin Naira domin kammala wani katafaren aikin ruwa da tsohuwar gwamnatin Jigawa ta fara
  • An fara aikin samar da ruwa ga mutanen jihar shekaru 24 da su ka gabata, amma gwamnoni bayan Saminu Turaki su yi watsi da shi
  • Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da ginin aikin da zai samar da ruwa akalla lita miliyan 10 ga mutanen Duste da kewaye

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Jigawa - Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar da ginin aikin samar da ruwan sha a Jigawa mai darajar N59.4bn wanda aka fara shekaru 24 baya.

A kaddamar da aikin ne a Siltilmawa da ke wani yanki a cikin karamar hukumar Ringim, kuma ya na daga cikin aikin ruwa mafi girma a jihar.

Kara karanta wannan

Zargin karkatar da N111.8bn: Majalisar wakilai ta shirya binciken gwamnatin Tinubu

Tinubu
Gwamnati za ta karasa aikin ruwa tsohuwar gwamnatin Jigawa Hoto: Garba Muhammad
Asali: Facebook

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an fara aikin ne a shekarar 2000, lokacin mulkin gwamnan Jigawa Saminu Turaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran aikin zai samar da lita miliyan 10 na ruwa a kullum don amfanin kusan miliyan 1.5 na al'ummar Dutse, babban birnin jihar.

Dalilan Tinubu na farfado da aikin ruwan Jigawa

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnatin tarayya ta dauki aniyar farfado da aikin samar da ruwa bayan gwamnatocin jihar sun gaza kammala babban aikin.

Shugaba Tinubu ya samu wakilcin Ministan albarkatun ruwa da tsabtace muhalli, Joseph Utsev ya ce;

“Shugaba Tinubu ya amince da samar da kudade don aiwatar da aikin. Wannan aikin ruwa wani muhimmin tsari ne wanda zai samar da ruwan sha mai tsafta ga mazaunan Dutse.

Lokacin kammala aikin ruwa a jihar Jigawa

Shugaban kasa ya amince da fiye da Naira biliyan 59.4 don gina wurin samar da ruwa wanda za a kammala a cikin watanni 24 a jihar Jigawa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya dura kan Tinubu, ya ce ba zai yi aiki da tsare tsaren 'T Pain' ba

A jawabinsa, gwamna Umar Namadi, ya ce kammala aikin zai habaka ci gaban Jigawa da kuma kasar, musamman a muradun samar da tsaftacen ruwan sha.

Jigawa: Gwamnati ta gano ma'aikatan bogi

A baya, kun ji cewa gwamnatin Jigawa karkashin jagorancin gwamna Umar Namadi ta bayyana cewa an bankado ma'aikatan bogi da ke karbar albashin akalla N3.6bn.

Gwamnatin Jigawa ta ce an gano ma'aikata 6,348 da ke karbar albashi duk wata ba bisa ka'ida ba ne bayan an kaddamar da tantance dukkanin ma'aikatan da ke yi mata aiki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.