Bayan Naja'atu Ta zargi Tinubu da Ware Arewa, An Dawo da Akanta Janar da Aka Sauke

Bayan Naja'atu Ta zargi Tinubu da Ware Arewa, An Dawo da Akanta Janar da Aka Sauke

  • Gwamnatin Tarayya ta bai wa Oluwatoyin Sakirat Madein damar ci gaba da rike kujerar Akanta Janar har zuwa watan Maris 2025
  • An dakatar da nadin Shemsudeen Babatunde Ogunjimi a matsayin Akanta Janar na rikon kwarya ba tare da wani karin bayani ba
  • Sauke Madein ya jawo barkewar rikici kan tsarin nada sabon Akanta Janar, inda wasu ke zargin saba doka wajen nadin Ogunjimi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa Oluwatoyin Sakirat Madein, da aka umarta a baya da ta yi ritaya, za ta ci gaba da rike kujerar Akanta Janar na Tarayya (AGF).

Rahotanni sun tabbatar da cewa Oluwatoyin Sakirat Madein za ta cigaba da rike matsayin har zuwa watan Maris na 2025.

Kara karanta wannan

Karancin takardan kudi: Kungiyar NLC ta dira a kan gwamnatin Bola Tinubu

Ogunjimi
Tinubu ya sauke Akanta Janar da ya nada makon da ya wuce. Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Daraktan Hulɗa da Manema Labarai na Ofishin Akanta Janar, Bawa Mokwa ya tabbatar da matakin ga Daily Trust ta wayar tarho.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

The Nation ta rahoto cewa an aikawa Madein da takarda daga Ofishin Shugaban Ma’aikata na Tarayya domin cigaba da aiki.

Rikicin nadin Akanta Janar na kasa

Rikici ya biyo bayan zargin rashin bin doka wajen nada Ogunjimi, wanda wasu ke cewa ba ya cikin wadanda suka cancanta su rike kujerar.

Bawa Mokwa ya bayyana cewa ba a ambaci cewa za a nada Ogunjimi ba a cikin takardar da aka aikawa Madein.

Fitacciyar ‘yar siyasa, Hajiya Naja’atu Mohammed ta yi zargin cewa an kauce wa doka wajen nada Ogunjimi, wanda a cewarta bai fi wasu manyan daraktocin da suka dace da matsayin ba.

“Akwai wasu daraktoci biyu daga Arewacin Najeriya, Danladi Comfort Zakowi da Luka Joshua, waɗanda suka fi cancanta a nada idan Madein ba ta nan.

Kara karanta wannan

Abin da Buhari ya ce bayan Wike ya kwace filinsa da na wasu manya a Abuja

"Amma, an tsallake su ba tare da bayani ba.”

- Hajiya Naja’atu Mohammed

Hajiya Naja’atu ta yi kira ga gwamnati da ta gyara kura-kuran da aka tafka domin tabbatar da zaman lafiya da gaskiya a tsarin shugabanci.

Tinubu zai raba tallafin 'yan majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan majalisar wakilai sun ce za su mika kudin da suka tara na watanni shida ga Bola Ahmed Tinubu.

A ranar 31 ga Disamba za a mika kudin ga Bola Tinubu domin ya raba su ga al'umma domin rage radadin cire tallafin man fetur da ya yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng