El Rufa'i Ya Fito da Dabarar Toshe Almundahana a Kasafin Kudi a Majalisa

El Rufa'i Ya Fito da Dabarar Toshe Almundahana a Kasafin Kudi a Majalisa

  • Dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa ya yi zargin cewa ana asarar kudin gwamnati ta abubuwan da ke kunshe a kasafin kudi
  • Ya ce abin takaici ne yadda ma'aikatu ke sanya kasafin abubuwa iri guda a kasafin kowace shekara da ake gabatar wa majalisa
  • Bello El Rufa'i ya zaburar da majalisa a kan yadda za ta magance asara kudaden jama'ar kasa ta hanyar kasafin hukumomin gwamnati

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja - Dan majalisar tarayya mai wakiltar Kaduna ta Arewa, Hon. Bello El Rufa'i ya bankado hanyar da majalisa za ta rage zurarewar kudin gwamnati.

Ya bayyana haka ne a zaman majalisar wakilai, inda ya ce akasarin abubuwan da ma'aikatu da hukumomin gwamnati ke sanya wa a kasafinsu, ba su da amfani

Kara karanta wannan

"Akwai lauje cikin nadi," Atiku ya zargi gwamnati da siyasantar da alkaluman NBS

Rufa'i
Dan majalisa na zargin ma'aikata da zurarar da kudin gwamnat Hoto; @B_ELRUFAI
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa bidiyon dan majalisar ya na neman a duba yiwuwar hana ma'aikatun bude hanyoyin wawashe kudaden al'umma.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisa na son dakile almundahana a gwamnati

The Cable ta ruwaito cewa Hon. Bello El Rufa'i ya nemi takwarorinsa da a rika sanya idanu a kan abubuwan da ke kunshe a cikin kasafin kudinsu.

Bello El-Rufa'i ya ce;

"Idan ka kalli ma'aikatun nan da ke zuwa da kasafin kudinsu, idan sun sayi ababen hawa a shekarar da ta gabata, su ajiye batun sake sayen wasu, motoci ba su tashi daga aiki haka nan."

Ya bayyana cewa irin wadannan abubuwa ya kamata majalisa ta rika dubawa domin toshe kafar zurarewar kudaden gwamnati.

"Majalisar tarayya ta sa ido," Bello El Rufa'i

Hon. Bello El Rufa'i ya bayyana cewa bai dace gwamnati ta dauko batun kudirin haraji ba, amma shugabanni su gaza daukar matakin rage kudaden da su ke kashewa.

Kara karanta wannan

Fafaroma ya fadi yadda ya tsallake harin kunar bakin wake sau 2 a kasar Iraqi

"Kasafin kudi a duk shekara su na zuwa da bukatar sayen sababbin kwamfuta, sababbin kayan kujerun ofis."

Dan majalisar ya bukaci majalisa ta tabbata hukumomin gwamnati ba su ci gaba da sayen kaya iri daya a kowace shekara ba, domin 'yan Njaeriya sun gaji.

Lauya ta ba dan majalisa hakuri

A wani labarin, kun ji cewa bayan dan majalisar Kaduna, Bello El Rufa'i ya yi barazanar garzaya wa kotu, lauyar da ake zargi da yada labarin karya ta nemi afuwa.

Sabina Nkiru Ezeoke ta farayada labarin cewa jai'an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC), ta kai samame gidan dan majalisar tare da kama miyagun kwayoyi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng